Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun kutsa har cikin fada, sun yi awon gaba da Basarake mai daraja

Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun kutsa har cikin fada, sun yi awon gaba da Basarake mai daraja

  • Yan bindiga sun sace wani babban basarake mai kima a fadarsa dake masarautar Mbutu, a jihar Imo ranar Alhamis
  • Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye bayanansa, yace maharan sun fasa fadarsa kafin su samu nasarar sace shi
  • Kakakin yan sandan jihar, Michael Abattam, yace tuni jami'an yan sanda suka bazama nemo maharan domin ceto sarkin

Imo - Wasu tsagerun yan bindiga kusan 10, ranar Alhamis ɗin nan, sun sace basaraken masaurautar Mbutu, karamar hukumar Aboh Mbaise, jihar Imo, mai suna Damian Nwaigwe.

Punch ta rahoto cewa maharan sun yi awon gaba da basaraken ne a cikin fadarsa da misalin ƙarfe 2:30 na daren Alhamis.

Wani mutumi daga cikin mazauna yankin, wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar da lamarin ga wakilan mu.

Jihar Imo
Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun kutsa har cikin fada, sun yi awon gaba da Basarake mai daraja Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Kara karanta wannan

Uwargida ta waskawa miji mari ana tsakiyar shirin ma'aurata a gidan Rediyo, bidiyo

Dailytrust ta rahoto Mutumin yace:

"An sace basaraken tsohuwar masarautar Mbutu dake karamar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo, Eze Damian Nwaigwe. An sace Sarkin mai daraja a fadarsa, da misalin karfe 2:30 na daren ranar Alhamis."
"Maharan da suka sace shi suna da yawa, sun zo a kan mashina kuma sun zarce 10. Sun wargaza fadarsa, suna harbi kan mai uwa da wabi, har saida suka samu nasarar tafiya da sarkin a ɗaya daga cikin abin hawan su."
"Masarautar sarkin tana gefen gari. Ya gina gidansa nesa da gidajen mutanen gari, hakan yasa ba zai zama abin wahala a sace shi ba tare da mutanensa sun kawo ɗauki ba."

Rahotanni sun bayyana cewa sace Sarkin mai daraja ya jawo tashin hankali a yankin, domin mazauna yankin sun gaza bacci tun lokacin da abin ya faru har zuwa wayewar gari.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sandan jihar Imo, Michael Abattam, ya tabbatar da sace sarkin lokacin da aka tuntuɓe shi.

Ya bayyana cewa tuni jami'an yan sanda suka bazama aikin nemo maharan, da nufin ceto sarkin ba tare da sun illata shi ba.

A wani labarin kuma Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi a jihar Zamfara

A cewar wasu mazauna yankin, yan bindigan sun ce zasu cigaba da kai hari kauyuka har sai gwamnati ta buɗe kasuwar dabbobi ta Shinkafi.

Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan wani harin sojin sama da ya hallaka iyalan Turji, yan bindigan dake karkashinsa suka cigaba da matsawa mutanen yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262