Mako Ɗaya Bayan Miƙa Rayuwarsu Ga Yesu, Matasa 2 Sun Kashe Fasto a Cikin Coci a Legas
- An kashe wani faston cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) mai suna Babatunde Dada
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu sabbin wadanda suka amshi addinin kirista ne suka kashe shi a ranar Talata 2 ga watan Disamba
- Daya daga cikin iyalan mamacin, Abolarinwa Olatunbosun, ya ce an shiga da rahoto wurin yan sanda kuma an kama daya cikin wanda ake zargin
Legas - Wasu sabbin tubabu sun kai wa wani fasto hari Babatude Dada na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) hari a garin FESTAC, da ke karamar hukumar Amuwo Odofin sun halaka shi.
The Punch ta ruwaito cewa an kashe faston ne a cikin cocin RCCG da ke 13 Road, 6th Avenue, FESTAC Town, a ranar Talata, 2 ga watan Disamba.
Sabbin tubabun biyu da aka ce sun kashe faston sun fara zuwa cocin ne a karon farko a ranar Lahadi da ta gabata.
Matasan biyu sun fito kan mimbari a yayin da ake wa'azi a coci sun mika rayuwarsu ga Yesu Almasihu.
Cocin ta basu wurin zama a harabar ta bayan sun yi ikirarin cewa ba su da wurin zama. Amma, bayan kimanin mako daya da basu wurin zaman, sun daba wa fasto wuka ya mutu.
Matar marigayin faston ta magantu
Da ta ke magana kan abin bakin cikin da ya faru, matar faston, Bose, ta ce ta kira mijinta a ranar da abin ya faru kuma ya yi mata alkawarin zai dawo gida ya huta.
Kalamanta:
"An kashe miji na ne a ranar 2 ga watan Disamba a coci. Shi ne mai kula da kudaden coci da gudanar da mulki, kuma shine faston cocin.
"Ba na tare da shi a lokacin da aka kashe shi, amma an fada min cewa sun karbi kudi daga hannunsa. Na ji cewa wadanda suka kashe shi sabbin tuba ne."
An kashe Fasto Dada ne bayan ya ciro kudi daga banki, an kama daya cikin wanda ake zargi
Kazalika, daya daga cikin yan uwansa, kuma kwararren masanin harkokin tsaro, Abolarinwa Olatunbosun, ya ce an kashe faston ne bayan ya ciro kudi daga banki.
Olatunbosun ya ce an shigar da rahoto wurin yan sanda, ya kara da cewa har sun kama daya daga cikin wadanda ake zargin bayan ya gudu Ilorin.
Amma, Kakakin yan sandan Jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, bai riga ya yi tsokaci kan lamarin ba.
Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba
A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.
‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.
Asali: Legit.ng