Nnamdi Kanu na jin azaba, yunwa yake ji sosai: Lauyansa ya bayyana

Nnamdi Kanu na jin azaba, yunwa yake ji sosai: Lauyansa ya bayyana

  • Nnamdu Kanu har yanzu bai samun abinda yake so a tsare hannun hukumar DSS a birnin tarayya Abuja
  • Lauyansa ya bayyana cewa sai ya kwashe kwana daya bai samu abinci ba
  • Wannan ya biyo bayan umurnin da kotu ta baiwa hukumar DSS na ta baiwa Nnamdi Kanu abinda yake so

Abuja - Lauyan Shugaban kungiyar masu neman kafa kasar Biyafara IPOB, Nnamdi Kanu, mai suna Ifeanyi Ejiofor ya koka kan yadda ake wahalar da shi a kurkukun hukumar DSS.

A jawabin da ya saki ranar Talata, Ejiofor ya bayyana cewa DSS bata bi umurnin da kotu ta bata makon da ya gabata ba.

Za ku tuna cewa a zaman kotu da akayi makon da ya gabata, Mai Shari'a Binta Nyako ta amsa bukatu biyar da lauyoyin Kanu suka gabatar.

Kara karanta wannan

Matashin Fasto ya yi garkuwa da babban Bishop na Katolika a jihar Imo

A cewar Ifeanyi Ejiofor sun shiga duba Nnamdi Kanu ranar Litinin, 6 ga Disamba don ganin halin da yake ciki.

Yace:

"Mun lura da cewa duk da umurnin da Mai Shari'a ta bada a kotu ranar 2 ga Disamba, 2021, DSS har yanzu bata daina samar umurni ba."
"Onyendu Mazi Nnamdi Kanu ya bayyana mana cewa babu ko daya cikin umurnin da akayi ranar 2 ga Disamba, 2021 da DSS ta bi."
"Ya bayyana mana cewa rabon da yaci abinci tun ranar Lahadi (Shekaran jiya)"

Nnamdi Kanu na jin azaba, yunwa yake ji sosai: Lauyansa ya bayyana
Nnamdi Kanu na jin azaba, yunwa yake ji sosai: Lauyansa ya bayyana Hoto: US
Asali: UGC

Ya kara da cewa ana cin zarafin Kanu ne saboda bukatar da lauyoyinsa suka gabatarwa kotu kuma ya lashi takobin kaiwa alkali kara.

"Ko shakka babu ana azabtar da shi ne saboda kukan da ya kaiwa kotu kan halin da yake ciki a tsare."

Kara karanta wannan

Jerin Abubuwa 5 da Kotu ta umurci DSS ta baiwa Nnamdi Kanu na walwala

"Gobe zamu garzaya kotu domin bayyana mata wannan abu saboda ba zamu lamunci haka ba."

Jerin Abubuwa 5 da Kotu ta umurci DSS ta baiwa Nnamdi Kanu na walwala

A cewar lauyansa:

"Kotu ta yanke cewa zata saurari dukkan bukatunmu a zama na gaba kuma ta bada wadannan umurni:

1. A baiwa Mazi Nnamdu Kanu walwalan da yake bukata a tsare

2. A baiwa Kanu damar canza riga

3. A bari Kanu yayi ibadun addininsa na yahudanci

4. DSS ta bari Kanu ya karbi duk bakon da yake so

5. A bari Nnamdi Kanu yayi hulda da sauran fursunoni dake wajen

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng