Mafarauta Da Ƴan Sa Kai Sun Ceci Matafiya Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane, Sun Kama 2
- Kungiyar hadakan ‘yan sa kai da mafarauta a ranar Lahadi sun dakatar da wasu masu garkuwa da mutane a babban titin Abuja zuwa Lokoja kuma sun yi ram da su
- ‘Yan bindigan sun yi yunkurin garkuwa da wasu matafiya ne a gadar Ahoko, su na gab da kai harin Allah ya turo ‘yan sa kai da mafarautan wadanda su ka yi gaggawar kai wa matafiyan dauki
- Daya daga cikin ‘yan sa kan ya shaida yadda suke tsaka da sintiri su ka hango mutane biyu cikin masu garkuwa da mutane su na yunkurin bude wa motar matafiyan wuta
Kogi - A ranar Lahadi hadakar ‘yan sa kai da mafarauta sun dakatar da wani hari da ‘yan bindiga suka kusa kai wa matafiya a daidai gadar Ahoko, kan babban titin Abuja zuwa Lokoja, Daily Trust ta ruwaito.
Daya daga cikin ‘yan sa kan wanda har da shi aka dakatar da harin ya shaida yadda su ka samu nasarar kama mutane biyu cikin ‘yan bindigan.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun boye ne gab da gadar, cikin hukuncin Ubangiji sai ga ‘yan sa kai da mafarautan.
A cewarsa:
“A ranar muna sintiri ne sai mu ka hango masu garkuwa da mutane su biyu sun bayyana su na yunkurin bude wa wata motar matafiya wuta, nan da nan mu ka dakatar da su.”
Daily Trust ta rahoto yadda ya ce masu garkuwa da mutanen sun kasa yin komai, hakan ya sa su ka yi gaggawar kama su.
Sauran ‘yan bindigan da suka boye sun tsere
Ya kara da cewa sauran ‘yan bindigan da su ka boye a cikin dajin da ke kusa da titin sun tsere bayan ganin an kama mutane biyun.
‘Yan sa kan sun ce yanzu haka masu garkuwa da mutanen da aka kama su na hannun hukuma a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Sannan yanzu haka an amshe bindigogi biyu daga hannunsu, har ila yau ‘yan sa kan da mafarautan su na ta duba dajin don binciko maboyarsu.
Kwamandan mafarautan jihar Kogi ya tabbatar da aukuwar lamarin
Kwamandan rundunar mafarautan jihar Kogi, Hassan Yakubu ya tabbatar da kamen ‘yan bindigan guda biyu a Ahoko, inda ya ce su na hannun jami’an tsaro.
Har lokacin rubuta rahoto, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, CSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran wakilin Daily Trust ba kuma bai bayar da amsar sakon da aka tura masa ba dangane da lamarin.
Mun Kashe Hakimi Don Yana Bincikar Shugaban Mu: Ɗan Ta'adda Da Suka Kashe Hakimin Ƴantumaki a Katsina
A wani labarin, Rundunar 'yan sanda a Jihar Katsina ta sanar da kama daya daga cikin 'yan bindigan da suka kai hari tare da kashe hakimin 'Yantumaki, Abubakar Atiku, da mai tsaronsa, Premium Times ta ruwaito.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan yayin da ya ke holen wanda ake zargin tare da wasu, a ranar Talata a Katsina.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta rahoto yadda 'yan bindiga suka kashe hakimin a ranar 1 ga watan Yunin 2020.
Asali: Legit.ng