Shugaba Buhari ya jajantawa iyayen daliban da suka mutu a hatsarin mota a Legas
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyaye da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin Legas
- Shugaban ya kuma yiwa gwamnati da al'ummar jihar jaje tare da yin addu'ar neman lafiya ga wadanda suka jikkata
- A jiya ne aka samu wani mummunan hatsarin babbar mota a jihar Legas, lamarin da ya tunzura matasa a yankin da abin ya faru
Abuja - Shugaba Buhari na Najeriya ya jajantawa iyayen daliban da hatsarin babbar mota ya afkawa a wani yankin jihar Legas.
A jiya ne aka samu afkuwar wani mummunan hatsarin babbar mota, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar dalibai biyu da jikkatar wasu 12.
Lamarin ya jawo nuna fushi daga wasu mazauna yankin, inda suka bukaci 'yan sanda su mika musu direban motar.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar ta hannun mai ba shugaban kasa shawara, Femi Adesina ya bayyana irin kaduwar da Buhari yayi da jin labarin.
A cewar sanarwar da Legit.ng Hausa ta gano a shafin Facebook ranar Laraba 8 ga watan Disamba:
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyaye, ‘yan uwa da abokan karatun daliban Ojodu Grammar School da suka rasa rayukansu a wani hatsarin da ya faru a ranar Talata a hanyar Isheri, Ojodu, a jihar Legas.
"Shugaba Buhari ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Legas da kuma mahukuntan makarantar Ojodu Grammar School kan rashin mai tsananin radadi wanda ya yanke rayuwar yara a wannan mummunan lamari.
"Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya ba iyaye da ‘yan uwa da ke cikin makoki hakuri a wannan lokaci na bakin ciki, ya kuma baiwa wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa."
Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar TalataRahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata
A baya kunji cewa, rundunar ‘yan sandan Legas ta ce dalibai biyu ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Ogunnusi, TheCable ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata wanda ya kai ga mazauna yankin suka rufe wani bangare na titin da tayoyi domin nuna adawa da hadarin.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata, Adekunle Ajisebutu, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, ya ce wasu mutane 12 sun samu raunuka a hadarin.
Asali: Legit.ng