Rashin Tausayi: Yadda 'yan bindiga suka kona fasinjoji 10 da ransu da tsakar rana a Sokoto
- ‘Yan bindiga sun banka wa ‘yan gudun hijira wuta inda suka kone su kurmus a kauyen Gidan Bawa da ke karkashin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto
- An samu bayanai akan yadda ‘yan gudun hijiran su ke hanyarsu ta zuwa Gadan Gayan da ke jihar Kaduna daga nan su zarce kudu don neman inda za su raba su ci gaba da rayuwa
- ‘Yan bindigan sun dana wa motarsu tarko ne inda su ka zagaye su kafin su bude mata wuta a cikin kauyen a ranar Litinin da misalin karfe 10 na safe
Jihar Sokoto - ‘Yan fashin daji sun babbaka wasu ‘yan gudun hijira a kauyen Gidan Bawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto da ransu, Daily Trust ta ruwaito.
An samu rahoto akan yadda suke hanyarsu ta zuwa Gadab Gayan da ke jihar Kaduna don zarcewa kudancin Najeriya su ci gaba da rayuwa.
Daily Trust ta bayyana yadda su ke cikin abin hawarsu ‘yan bindigan su ka yi musu zobe tare da bude musu wuta.
Lamarin ya faru ne ranar Litinin da safe
Lamarin ya faru ne a kauyen Teke da ke karkashin Gidan Bawa da misalin karfe 10am na safiyar Litinin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta shaida cewa:
“Yan bindigan sun dinga harbin tayoyin motar, wanda ya ja motar ta dungura ta fara ci da wuta.”
An samu bayanai akan yadda ‘yan bindigan su ka zagaye motar sai da suka tabbatar babu wani fasinja da ya rayu.
Daya daga cikin ‘Yan sa kan karamar hukumar Sabon Birni ya sanar da manema labarai cewa ‘yan gudun hijiran daga kusa da Jamhuriyar Nijar su ke.
A cewar majiyar:
“Su na hanyarsu ta wucewa kudu ne don samun tudun rabewa mummunan lamarin ya auku.”
Sojoji ba sa yin komai akan hare-haren
Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa su goma ne fasinjojin kuma duk sai da suka rasa rayukansu.
Dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta kudu, Ibrahim Sa’idu ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace yanzu fashin babura, wayoyi da tsadaddun abubuwa ‘yan bindiga suke yi.
A cewarsa har garkuwa su ka yi da mutane tara a kauyen Masawa kwanan nan.
Wani mai gadi ya ce sojoji ba sa yin komai akan hare-haren da ake kai wa yankin.
Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaron kasar nan da su kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a kasa musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis bayan wani taro da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaron kasa, NSC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa shugaban kasan ya ba ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro ciki har da jami’an binciken sirri umarnin kada su zauna har sai sun kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, amsar kudaden fansa da sauransu a Najeriya.
Asali: Legit.ng