An kama wani soja da budurwarsa ɗauke da harsashi fiye da 90 a Borno
- Yan sanda sun yi holen wata mata da aka kama dauke da harsashi fiye da 90 cikin wata jaka a Askira, Jihar Borno
- An kama matar ne bayan ma'aikata a tashar motar sun tambaye ta abin da ke cikin jakar ta nuna bata sani ba sai suka umurci ta bude
- Bayan ta bude sai aka gano harsashi fiye da 90 nan take suka tarkata ta zuwa hedkwatan yan sandan inda ta ce saurayinta soja ne ya aike ta
Borno - Yan sanda a jihar Borno sun yi holen wata mata, Anita Yohanna, wacce aka kama dauke da harsashi za ta shiga motar haya daga garin Askira zuwa Yola, a karamar hukumar Askira a jihar Borno.
Matar, mai shekaru 25 ta yi ikirarin cewa wani saurayinta soja ne, Lance Kofur Aliyu Isa, ya bata domin ta bawa wani direban motar haya da zai ta fi Yola, The Punch ta ruwaito.
Ta ce:
"Mun shafe kimanin shekara daya da wata hudu muna soyayya yanzu. Sunansa Aliyu Isa, Lance Kofur ne a Rundunar Sojojin Najeriya, yana aiki a Askira. Ya bani jakar ya ce in kai tasha a Uba in bada a kai masa Yola.
"Na isa tashar misalin karfe 5 na yamma. Da na isa, direban ya tambaye ni abin da ke ciki, na fada masa ban sani ba. Daga nan, ya ce in bude domin mu tabbatar kafin ya karba. Da muka bude sai muka gano harsashi ne guda 90; daga nan aka kama ni aka kai ni hedkwatan yan sanda."
Yohanna ta kara da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun kama sojan sun tsare shi kamar yadda ya zo a ruwayar The Punch.
A bangarensa, Kwamishinan yan sandan jihar Borno, Abdu Umar, ya ce wannan kamen daya ne daga cikin da dama da suke bincike a kai.
Ya ce rundunar yan sandan kuma tana bincike a kan wani rahoton sata, cin zarafin yara da lalata wayoyin wutar lantarki na gwamnati.
Umar ya bada tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin da zarar an kammala bincike.
Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai
A wani labarin mai alaka da wannan, Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojoin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.
Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.
Asali: Legit.ng