Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya taya ministansa murnan cika shekaru 70

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya taya ministansa murnan cika shekaru 70

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu murnar cika shekaru 70 a duniya
  • Shugaban ya bayyana haka ne ta hannun mai bashi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina yau Talata
  • Shugaban ya kuma yaba wa Lai Mohammed da irin kokarin da yake na kawo sauyi mai kyau a Najeriya

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu na Najeriya murnar cika shekaru 70 a duniya.

Cikin wata sanarwa da mashawarcin Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar kuma Legit.ng Hausa ta samo a yau Talata 7 ga watan Disamba, ya ce shugaban ya kuma yaba da irin kokarin da Lai Mohammed ke yi a gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

Buhari ya kori shugabannin wutan lantarki a Abuja saboda yajin aikin ma’aikata

Hakazalika, ya kuma yaba masa da kasancewa jajirtacce wajen yiwa kasa, kama daga aiki a matsayin lauya har zuwa zama dan jam'iyyar APC mai kishi.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya taya ministansa murnan cika shekaru 70 | Hoto: saharareporters.com
Asali: Depositphotos

Sanarwar ta kara da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A matsayinsa na jigon jam’iyya, shugaba Buhari ya lura da sadaukarwa da gudunmawar da ministan ya bayar wajen samar da manyan nasarori na yada labarai da suka yi tasiri wajen kawo sauyi a kasar.
"Shugaban ya yi imanin cewa Mohammed yana aiki tukuru don samar da fahimta da kuma inganta martabar kasar ta hanyar dinke baraka a fannin bayanai, tare da yaba wa hazakarsa, juriya da kaifin hankalinsa.
"Shugaba Buhari ya bi sahun mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da jam’iyyar APC da kuma masana’antar yada labarai wajen yi wa ministan yada labarai fatan kasancewa lafiya, karin karfi da tsawon rai."

Kara karanta wannan

Ku kara kaimi wajen fatattakar yan ta'adda a Najeriya, Shugaba Buhari ga Sojoji

An nada shugaba Buhari shugabancin wata babbar kungiya a Afrika ta PAGGW

A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Pan African Great Green Wall (PAGGW), a Afirka, kamar yadda karamar minista a ma'aikatar muhalli, Mrs Sharon Ikeazor, ta sanar a ranar Lahadi a Abuja.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Sagir el Mohammed ya fitar ta ce Najeriya ta karbi ragamar mulkin ne a karshen taron shugabannin kasashe da gwamnatocin PAGGW karo na 4 da aka gudanar a ranar 2 ga watan Disamba a Abuja.

A cewar ministar:

“A karshen taro na 4 na CHSG, Najeriya ta karbi shugabancin kungiyar PAGGW."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.