Iyayen yara 8 da aka tsinci gawarwakinsu a wata mota sun yi martani kan lamarin
- Iyayen yaran da aka samu gawarwakinsu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a Legas sun yi magana game da wannan mummunan lamari
- Ibrahim Jubril, daya daga cikin iyayen da suka rasa ‘ya’ya hudu, ya ce babu wanda ya san yadda yaran suka shiga cikin motar
- Jubril da wani mahaifi, Isiaka Abdul-Wahab sun ce sun mika kaddarar ga Allah kasancewar shi ne mai bayarwa da karbewa
Jihar Legas – Ibrahim Jubril, daya daga cikin iyayen da aka tsinci gawar ‘ya’yansu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a Legas, ya magantu kan wannan mummunan lamari.
Idan za a iya tunawa, an tsinci gawarwakin yara takwas da aka ce ‘yan shekara hudu zuwa shida ne a cikin wata mota da aka ajiye a kan titin Adelayo, Jah-Michael, a yankin Badagry a Legas, a ranar Asabar, 4 ga watan Disamba.
Da yake magana game da lamarin, Jubril wanda ya rasa ‘ya’ya hudu maza biyu mata biyu, ya ce babu wanda ya san yadda yaran suka shiga cikin motar, inji rahoton The Cable.
Mahaifin yaran hudu ya ce yana cikin masallaci kwatsam aka kira shi ya zo ya ga abin da ya faru da 'ya'yansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
“Ina cikin wannan babban masallacin sai mutane suka zo kirana don in zo in ga abin da ya faru da ‘ya’yana.
“Kafin na isa wurin, sun fito da su daga motar. Babu wanda ya san yadda suka shiga cikin motar suka kulle kansu a ciki.
“A matsayinmu na musulmi, duk abin da ke faruwa a rayuwa daga Allah yake, mun yi imani cewa Allah ne yake bayarwa da karbewa a kowane lokaci a rayuwa. Ita kuma matata ta mika kaddara ga nufin Allah.
"Mun yi jana'izar 'ya'yanmu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada kuma muna nan a masallaci muna addu'ar Allah ya gafarta musu zunubansu."
Wani mahaifi shi ma ya magantu kan lamarin
Haka kuma, Isiaka Abdul-Wahab, wanda ya rasa ‘ya’ya uku a lamarin, ya ce ya mika kaddara ga nufin Allah, inji rahoton Premium Times.
Yace:
“Yarana biyu, Abdul-Wahab da Yakubu, sai yarinya, Zainab, sun dawo daga makarantar Al-Qur’ani. Bayan sun ci abinci ne suka fara wasa da abokansu.
“Na tafi masallaci ina sallah na kusan awa daya, daga nan na tafi makarantar Al-Qur’ani don ganawa da wani abokina.
“Ba zato ba tsammani, matata ta aika a kira ni. Da na isa wurin sai na ga gawarwakin ’ya’yana babu rai.
"Mun mika kaddara ga yardar Allah domin shi ne mai bayarwa da karba".
A tun farko, kunji cewa, an tsinci gawarwakin wasu yara takwas a cikin wata mota da aka ajiye akan titin Adelayo, Jah-Micheal a Badagry ta jihar Legas.
An ce yaran suna tsakanin shekaru hudu zuwa shida, inji rahoton TheCable.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 4 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng