Daga dawowar Buhari, Shima Osinbajo ya shilla Dubai don halartan taron iskar Gas na girki LPG

Daga dawowar Buhari, Shima Osinbajo ya shilla Dubai don halartan taron iskar Gas na girki LPG

  • Kwana daya da dawowar Buhari daga Dubai, mataimakinsa ya hau jirgi zai yi nasa tafiyar birnin
  • Jawabi daga ofishin Osinbajo ya nuna cewa mataimakin Buharin zai tafi halartan taron makamashi ne
  • Shugaba Buhari ya dawo Najeriya ranar Lahadi bayan kwanan hudu da Dubai da Abu Dhabi

Abuja - Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tashi daga Abuja inda ya nufi birnin Dubai, hadaddiyar daular Larabawa UAE yau Litinin, 6 ga Disamba, 2021.

A cewar mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, mai gidansa ya tafi Dubai ne halartan taron kungiyar iskar Gas na girki.

Ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin a birnin tarayya Abuja, rahoton TVC.

Shima Osinbajo ya shilla Dubai
Daga dawowar Buhari, Shima Osinbajo ya shilla Dubai don halartan taron iskar Gas na girki LPG Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Annobar Korona ta kawo min cikas wajen yaki da rashawa da matsalar tsaro, Buhari

A cewarsa, Osinbajo ya gabatar da jawabi a wannan taro da za'a kwashe kusan mako guda ana yi kuma manyan Ministocin kasashen duniya zasu hallara.

Ya kara da cewa sama da mutum 2,000 daga kasashe 72 zasu halarci taron.

Taron iskar gas WLPGA na gudana shekara bayan shekara tun da aka fara a birnin Amsterdam a shekarar 2019.

Jawabin ya kara da cewa mataimakin Shugaban kasan zai dawo Najeriya ranar Alhamis.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Dubai

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya dawo birnin Dubai, hadaddiyar daular Larabawa da bayan kwanaki hudu don halartan taron baja kolin EXPO 2020.

Buhari ya dira filin jirgin Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja ne da yammacin Lahadi, 5 ga watan Disamba, 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng