Hukumar jami'a ta kori lakcarorinta 4 bisa karbar kudi ta bayan fage da rashin da'a
- Wata jami'ar jiha a jihar Edo ta sallami wasu ma'ikatanta bisa zargin karbar kudi ba bisa ka'idar jami'ar ba
- An bayyana korarsu daga ranar 1 ga watan Disamba, inda hukumar jami'ar ta tabbatar da haka bayan tuntubanta
- A bangaren lakcarorin, har yanzu dai ba a samu jin ta bakin ko daya daga cikinsu ba, don bayyana martani bisa korar
Edo - Hukumar gudanarwar jami’a mallakin jihar Edo ta Ambrose Alli (AAU) da ke Ekpoma, ta amince da korar wasu lakcarorin jami’ar guda hudu bisa zarginsu da rashin da’a.
An amince da korar tasu ne a taron gaggawa na kungiyar shiga tsakani na musamman (SIT), wanda aka gudanar a ranar Laraba 1 ga Disamba, 2021.
A taron na gaggawa, an yi la’akari da rahoton kwamitin ladabtarwa na manyan ma’aikata (SSDC) kan zargin da ake yi wa lakcarori hudu da aka kora.
An sallame su daga hidimar jami’ar ne bisa zargin karbar kudade ba bisa ka’ida ba, da sauya sakamakon dalibai da wasu munanan ayyuka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jerin lakcarorin da aka kora da tsangayoyin da suke aiki
- Barr. Patrick Ikechuckwu Iweoha (Tsangayar shari'a)
- Engr. Dr Lawrence Imaekhai
- Engr. Dr Sumaila Jimoh (Tsangayar injiniyanci da fasaha)
- Engr. Haruna Andrew Idoko (Masanin Fasaha a tsangayar injiniyanci da fasaha)
A cewar rahoton daga jami'ar:
"Saboda haka, an kori ma'aikatan da ke sama saboda rashin da'a wanda ya fara aiki daga ranar Laraba 1 ga Disamba, 2021."
Da yake tabbatar da korar lakcarorin ga jaridar PM News ta wayar tarho, Jami’in Hulda da Jama’a/Mukaddashin Magatakarda na AAU, Edward Aihevba, ya ce:
“Eh, an kori lakcarorin hudu ne saboda rashin da’a.”
Ba a dai iya samun jin ta bakin ko da daya daga cikin lakcarorin da aka kora ba.
Lakcaran Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da dalibansa mata
A bangare guda, Jami'ar jihar Kwara dake Malete, ta sallami daya daga cikin lakcarorinta, Pelumi Adewale, bisa zargin yunkurin lalata da ɗalibarsa, Tosin Adegunsoye.
Mataimakin shugaban KWASU, Mustapha Akanbi, shine ya bayyana haka a Ilorin ranar Litinin, yayin da yake fira da manema labarai kan bikin yaye ɗalibai karo na 8 da 9.
Akanbi yace tsohon lakcaran ya yi amfani da kasancewarsa daya daga cikin lakcarorin jami'ar KWASU wajen bata mata suna a idon mutane, kamar yadda Punch ta ruwsito.
A wani labarin na daban, wani malami a kwalejin fasaha dake Offa, jihar Kwara, Mista Ayatu Ikani, ya rigamu gidan gaskiya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Mista Ayatu ya yanke jiki ya fadi yayin da suke cikin taro da mutanensa a Offa, jihar Kwara.
Duk wani kokari da mutanen yankinsa za su yi na ganin ya farfardo, sun yi amma ba su samu nasara ba saboda lokacinsa ya yi.
Asali: Legit.ng