Hotuna cikin labari: Alaramma Ahmad Sulaiman ya shiga ofis, ya mika godiya ga Allah
- Alaramma Ahmad Sulaiman ya shiga ofishinsa bayan nadin da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa matsayin kwamishinan ilimi na biyu
- Fitaccen malamin kungiyar izalan ya wallafa hotunansa a sabon ofishinsa inda ya sanar da cewa yau ya shiga ofis a matsayin kwamishina
- A saman hotunansa da ya wallafa, ya mika godiyarsa ga Allah tare da yin barar addu'o'i daga bakunan jama'a masu albarka
Kano - Bayan nada Alaramma Ahmad Sulaiman da gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi a matsayin kwamishinan ilimi na biyu na jihar Kano, Malamin ya shiga ofishinsa a ranar Litinin.
Alaramman ya wallafa hotunansa tare da mika godiya ga Allah a yau Litinin inda ya sanar da cewa ya shiga ofishinsa.
Kamar yadda malamin kuma kwamishinan ilimi na jihar Kano na 2 ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga hotunansa tare da Sheikh Abdallah Gadon Kaya a sabon ofishin nasa.
Sabbin hotunan El-Rufai inda ya ɗau wankan jins tamkar wani saurayi yayin da ya fita duba wasu ayyukan jiharsa
Kamar yadda yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Alhamdulillah, yau na shiga ofis di na. Ina rokon Allah ya ba ni ikon yin adalci akan kowa. Ina bukatar addu'o'in ku."
Ganduje ya nada Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi 2
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada Sheikh Alaramma Malam Ahmad Sulaiman Ibrahim kwamishinan ilimi na biyu a jihar.
Kamar yadda Alaramman ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya mika godiya ga Allah madaukakin Sarki tare da mika godiya a madadinsa da iyalansa ga Gwamnan.
Kamar yadda wallafar tace:
"Godiya ta tabbata ga Allah. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki. Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammadu S. A. W.
"Bayan haka, a madadina da na iyalaina da al'ummar da ta ke tare da mu, muna mika godiya mai tarin yawa ga mai girma Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduja, Khadimul Islam, bisa nada ni da yayi a kwamishina na 2 a hukumar ilimi ta jihar Kano.
"Ina rokon Allah ta'ala ya sanya alheri, yasa mana albarka cikin wannan kujera da ya ba mu dan ya jarabce mu."
Asali: Legit.ng