'Yan sanda sun fattataki 'yan bindiga, sun ceto wani matashi dan shekara 17 a Kaduna

'Yan sanda sun fattataki 'yan bindiga, sun ceto wani matashi dan shekara 17 a Kaduna

  • Zaratan jami'an yan sanda a Jihar Kaduna sun ceto wani matashi, Sani Adams, da masu garkuwa suka sace a Kaduna
  • Adams ya tafi gonar shinkafa ne a kusa da kauyen Afaka yana aiki a yayin da miyagun masu garkuwan suka yi awon gaba shi
  • Bayan musayar wuta tsakaninsu, yan bindigan sun tsere da raunukan harsashi sun saki yaron inda daga bisani aka kai shi asibiti

Vanguard ta rahoto 'yan sanda a jihar Kaduna sun ceto wani yaro dan shekara 17 da yan bindiga suka sace a wani gonar shinkafa da ke bayan gari.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige a ranar Asabar ya tabbatar da ceto yaron dan shekara 17.

Kara karanta wannan

Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa

'Yan Sanda sun fattataki 'yan bindiga, sun ceto wani matashi dan shekara 17 a Kaduna
Yan sanda sun ceto matashi dan shekara 17 daga hannun masu garkuwa a Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce misalin karfe 2 na ranar 4 ga watan Disamban 2021, jami'an su da ke sintiri a Dajin Sabon Birni sun ji karar harbin bindiga sai suka shiga dajin don ganin abin da ke faruwa.

Ya ce:

"Jami'an mu sun shiga dajin suka yi musayar wuta da masu garkuwar. Yayin arangamar da bata garin, an ceto wani yaro mai shekaru 17, Mr Sani Adams.
"Yan bindigan sun tsere da raunin harsahi. An kai Sani Adams cibiyar lafiya ta Kutungare domin duba lafiyarsa.
"An sace shi ne yayin da ya ke aiki a gonar shinkafa da ke kusa da kauyen Afaka a Kaduna. Mun sake bincika dajin sosai don ganin ko za mu ceto wasu tare da fatattakar miyagun."

Hakazalika, rahoton ya ce kakakin yan sandan ya shawarci al'umma kar su karaya saboda afkuwar wannan lamarin kwara daya, su kuma rika kai rahoton duk wanda aka sace a yankunansu.

Kara karanta wannan

Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda

Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaron kasar nan da su kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a kasa musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis bayan wani taro da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaron kasa, NSC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa shugaban kasan ya ba ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro ciki har da jami’an binciken sirri umarnin kada su zauna har sai sun kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, amsar kudaden fansa da sauransu a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164