Innalillahi: Tsohon Minista a Najeriya, Sherrif, ya rigamu gidan gaskiya
- Tsohon ministan tarayyan Najeriya a zamanin mulkin Janar Badamasi Babangida, Bunu Sherrif Musa, ya rigamu gidan gaskiya
- Tsohon ministan ya jagoranci ma'aikatun gwamnatin tarayya da suka haɗa da ma'aikatar Lantarki, hakar ma'adanai da cigaban ƙarafa
- Sakataren kungiyar dattawan jihar Borno, Dakta Bulama, yace wannan rasuwa ta zo musu bagatatan, mutum 2 kenan cikin kankanin lokaci
Borno - Tsohon minista a Najeriya, karkashin mulkin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Injiniya Bunu Sheriff Musa, ya kwanta dama ranar Lahadi.
Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa tsohon ministan ya mutu ne yana da shekaru 74 a duniya.
Bunu ya rike mukamin ministan a ma'aikatun gwamnatin tarayya daban-daban, da suka haɗa da, haƙar ma'adanai, wutar lantarki da kuma ma'aikatar cigaban ƙarafuna.
Hakanan kuma kafin rasuwarsa, Bunu Sherrif Musa, ya rike mukamin jakadan Najeriya a ƙasar Faransa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dattawan Borno sun tabbatar
Da yake tabbatar da rasuwar tsohon ministan, sakataren kungiyar dattawan Borno, Dakta Bulama Mali Gubio, yace rasuwarsa ta barmu cikin takaici
Sakataren yace:
"Muna cikin jimamin rasuwarsa, shi mutumin kirki ne. Muna tare da shi a fadar mai martaba Shehun Borno kwanaki biyu da suka gabata."
"Amma ba mu san cewa kwanakin sa na gab da ƙarewa ba, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Rasuwarsa ta zo kwanaki kaɗan bayan wani dattijon Borno ya mutu, Alhaji Tijjani Bolori."
"Muna Addu'a Allah SWA ya karbi bakuncin ran su, ya kuma saka musu da gidan Aljanna bisa kyakkyawan ayyukan da suka yi a rayuwarsu."
A wani labarin na daban kuma Matasan jihar Kaduna sun fusata, Sun aike da kakkausan sako ga miyagun yan bindiga
Matasan Kudancin jihar Kaduna sun bayyana cewa lokaci ya yi da zasu tashi tsaye wajen kare yankunan su daga ta'addanci.
Matasan yankin karkashin kungiyar mutanen kudancin Kaduna,ɓSOKAPU, sun sha alwashin kare kan su da yankinsu daga ta'addancin yan bindiga.
Asali: Legit.ng