Najeriya na iya ballewa ma kafin zaben 2023, Cardinal Onaiyekan
- Babban Limanin Katolika ya bayyana ra'ayinsa game da matsalar tsaron da Najeriya ke fama da ita
- Cardinal Onaiyekan ya bayyana cewa idan ba'a magance matsalar tsaro ba, da alamun Najeriya ta watse kafin 2023
- A cewar, Shugabannnin Najeriya kawai marasa tunanin ne masu maitan mulki da kujeran iko
Abuja - Tsohon Shugaban Cocin Katolikan Abuja, John Cardinal Onaiyekan, ya bayyana cewa da yiwuwan Najeria ta balle kafin 2023 saboda halin da kasar ke ciki.
Ya bayyana cewa Shugabannin Najeriya na son mannewa kan kujeran mulki ko da wa'adinsu ya karewa saboda son kai, mugunta da rashin tunani.
A hirar da yayi da jaridar Saturday Punch, Shehin Malamin ya bayyana cewa daya daga cikin abubuwan dake barazana ga Demokradiyya a Najeriya shine Gwamnatocin dake ci basu son zaben gaskiya da lumana.
A cewarsa:
"Babu wani dalilin da zai sa a cigaba da fuskantar matsalar tsaro har 2023. Idan ko ba'a shawo kan matsalar ba, hakan na nufin mun jji kunya a matsayin al'umma kuma babu bukatar wani zabe kasar ta watse."
"Game da zaben kuwa, bamu da tabbacin Najeriya ba zata balle ba. Wadannan matsaloli (na tsaro) ya kamata mu fuskanta yanzu."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Almajiranci ke ruruta wutan rashin tsaro a Arewacin Najeriya, Bishop Onaiyekan
A wani labarin kuwa, Cardinal John Onaiyekan, ranar Asabar ya bayyana cewa Almajiranci ne abinda ke ruruta wutan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.
Onaiyekan ya bayyana cewa yaran da iyayensu suka mance da su shekarun baya ne suka zama yan ta'addan Boko Haram.
Punch ta ruwaito cewa Cardinal John Onaiyekan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron kaddamar da fim dake wayar da kai kan kananan yara marasa gata.
A cewarsa:
"Muna da babbar matsala yanzu a Arewa na Almajiranci. Wadannan kananan yara ne musamman wadanda iyayensu suka yi watsi da su. Mun san da yawa cikinsu sun zama yan Boko Haram."
Asali: Legit.ng