Danzago ne Shugaban APC a Kano: Gwamna Badaru da Gwamnan Ekiti sun shaida

Danzago ne Shugaban APC a Kano: Gwamna Badaru da Gwamnan Ekiti sun shaida

  • Rikicin jam'iyyar APC a Kano tsakanin bangaren Gwamna da Sanata Shekarau ya ki ci, ya ki cinyewa
  • Mai Shari'a Hamza Mua'zu na kotun tarayya ya soke dukkan shugabannin jam'iyyar APC na bangaren Ganduje

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru sun shaida cewa Ahmadu Haruna Zago (Danzago) ne shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Kano.

Kayode Fayemi ya ambaci Danzago matsayin Shugaban APC a Kano ne a taron lakca da aka shirya don murnar cika shekaru 21 da kafa cibiyar ilmin demokradiyya dake jami'ar Bayero BUK.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan shine karo na farko da za'a ambaci Danzago matsayin Shugaban APC.

Zaku tuna cewa a ranar 18 ga watan Oktoba, an gudanar da zabukan shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Abdullahi Abbas, Sule Garo da wasu yan siyasa 5 suka dau nauyin kaiwa ofishinmu hari: Shekarau

Amma sakamakon rabuwar kai da ya auku tsakanin 'yayan jam'iyyar inda aka rabe biyu; Malam Ibrahim Shekarau tare da mabiyansa sun gudanar da nasu zaben daban yayinda Gwamna Ganduje ya gudanar da nasu daban.

Yayinda aka zabi Alhaji Abdullahi Abbas matsayin shugaban tsagin Ganduje, an zabe Ahmad Harun Zago matsayin Shugaba na tsagin Shekarau.

Daga baya uwar jam'iyya ta bayyana cewa tana tare Abdullahi Abbas da tsagin Ganduje.

Danzago ne Shugaban APC a Kano: Gwamna Badaru da Gwamnan Ekiti sun shaida
Danzago ne Shugaban APC a Kano: Gwamna Badaru da Gwamnan Ekiti sun shaida
Asali: Facebook

Shekarau ya shiga kotu

Sakamakon haka tsohon Gwamnan Kanon ya shigar da kara kotu don sanin wanda ke da gaskiya.

Wadanda suka kai karar sun hada da Senator Shekarau (Kano ta tsakiya), Senator Barau (Kano ta Arewa), ;Nasiru Abdua, Tijjani Abdulkadir Jobe, Shaaban Sharada, da Haruna Isa Dederi.

Kotu ta yanke hukunci

Kara karanta wannan

Matashin zai auri mata biyu rana guda bayan dirka musu ciki

Babbar kotu mai zamanta a Abuja karkashin Mai Shari'a Hamza Mua'zu ta soke dukkan shugabannin jam'iyyar All Nigeria Peoples Congress da ke biyayya ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Da ya ke yanke hukuncin a ranar Talata, alkalin ya amince ce bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ne halatattun zababun shugabanni.

Ya ce tsagin Gwamna Ganduje ba su yi zabe a matakin mazabu ba da kananan hukumomi.

Rikicin APC a Kano: Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu na rushe zaɓen ɓangarensa

Antoni Janar kuma kwamishinan Shari'a na jihar Kano, Musa Lawan, ya ce za su daukaka kara bisa hukuncin da kotun tarayyar ta yanke, rahoton Premium Times.

Mr Lawan ya ce gwamnatin tana nazarin hukuncin kafin ta dauki matakin ta na gaba.

Ya ce:

"Muna nazari kan hukuncin domin mu gani ko kotun tana da ikon sauraron karar tunda farko."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng