Da Ɗuminsa: Gwamnatin jihar Legas ta rufe wata makaranta kan mutuwar ɗalibi
- Ma’aikatar ilimi ta jihar Legas ta rufe kwalejin Dowen ta Lekki Phase 1 don samun damar yin bincike akan mutuwar wani dalibi, Sylvester Oromoni Jnr
- Duk da dai ‘yan uwan dalibin sun yi zargin ya rasu ne bayan wani dalibi ya dake shi har da ji masa raunuka saboda ya ki shiga wata kungiyar asiri
- An rufe makarantar ne bayan kwamishinan ilimin jihar, Mrs Folasade Adefisayo da sauran ma’aikatan ma’aikatar ilimi sun kai ziyara makarantar ranar Juma’a
Legas - Gwamnatin jihar ta rufe Kwalejin Dowen ta Lekki Phase 1 don samun damar bincike akan mutuwar wani dalibi, Sylvester Oromoni Jnr, wanda ake hasashen ya mutu ne sakamakon wata kungiyar asiri a ranar Talata.
Rufe makarantar ya biyo bayan ziyarar da kwamishinan ilimin jihar, Mrs Folasade Adefisayo da sauran manya na ma’aikatar ilimin su ka kai makarantar ranar Juma’a, The Nation ta ruwaito.
‘Yan uwan yaron sun yi zargin ya mutu ne sakamakon raunukan da wani dalibi ya ji masa saboda tsananin duka akan kin amincewarsa da shiga wata kungiyar asiri.
The Nation ta ruwaito yadda hukumar makarantar ta ce yaron ya samu raunukan ne yayin da yake buga kwallo.
Gwamnatin jihar za ta dage wurin bincike akan lamarin
A wata takarda wacce mataimakin kakakin ma’aikatar ilimin jihar Legas, Mr Ganiu Lawal ya saki, ta bayyana cewa:
“Gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarnin rufe kwalejin Dowen da ke Lekki ba tare da bayar da ranar komawa ba don yin bincike akan mutuwar Sylvester Oromoni Jnr, dalibin makarantar.
“Kwamishinan ilimin jihar, Mrs Folasade Adefisayo ta sanar da rufe makarantar bayan kammala taro da hukumar makarantar da malaman.
“Kwamishinan ta bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa, inda ta ce za a yi bincike mai zurfi akan tushen lamarin.”
Dama kwamishinan ta yi ta’aziyya ga ‘yan uwan mamacin
A wata takarda wacce kwamishinan ta saki a baya ta yi wa ‘yan uwan Sylvester ta’aziyya.
Gwamnatin jihar Legas ma ta tura sakon ta’aziyyarta ga iyayen Sylvester Oromoni Jnr mai shekaru 12, dalibin Kwalejin Dowen da ke Lekki.
Har ila yau, Kwamishinan ta kwatanta lamarin a matsayin abu mai firgitarwa kuma a cewarta babbar asara ce ga jihar.
Gwamnatin jihar Legas za ta tsaya tsayin-daka wurin kare hakkin yara
Gwamnatin jihar Legas za ta ci gaba da tuntubar iyayen yaron a wannan lokaci da suke cikin radadi, kamar yadda ta shaida.
Kwamishinan ta kara da cewa sai sun tabbatar wa ‘yan uwan marigayi Sylvester Oromoni Jnr da duk wasu ‘yan Legas kokarinsu na ganin sun gano tushen lamarin, sannan gwamnatin jihar za ta tabbatar ta ci gaba da kare hakkin yara.
Asali: Legit.ng