Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu
- DPO na yan sandan Furgar ya samu yanci bayan kwashe kwanaki shida hannun masu garkuwa da mutane
- Yan bindigan sun tare shi a hanya a watan Nuwamba yayinda dogarinsa ya gudu
- Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun kira iyalinsa kuma sun bukaci kudin fansa milyan hamsin
Babban jami'in dan sanda kuma DPO na garin Fugar, karamar hukumar Etsako Central a jihar Edo, CSP Ibrahim Ishaq, ya shaki kamshin yanci bayan kimanin mako guda hannun yan bindiga.
Rahotanni sun nuna cewa an saki DPOn ne da daren Alhamis, 2 ga Disamba, 2021.
Kakakin yan sandan jihar Edo, Bello Kongtons, ya tabbatar da sakin DPOn amma bai yi tsokaci kan ko an biya kudin fansa ba.
Yace:
"Ina mai tabbatar da cewa jami'an tsaro sun ceto DPO na Fugar daga hannun yan bindiga."
A baya mun kawo muku cewa DPO na ofishin Fugar dake jihar Edo, CSP Ibrahim Aliyu Ishaq, yayi arangama da tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Edo.
PRNigeria ta ruwaito cewa yan bindigan sun yi awon gaba da shi ne kusa Rafin Ise dake tsohuwar hanyar Auchi-Ekperi-Agenebode ranar Juma'a.
Rahoton ya kara da cewa tuni sun tuntubi iyalansa kan maganar kudin fansansa.
Gabanin komarwa Edo, CSO Ishaq yayi DPO a ofishin yan sandan Dakata a jihar Kano.
A riwayar Solacebase, yan bindiga sun bukaci kudi N50m kafin su sake shi.
Asali: Legit.ng