Bayanan kudin Abacha da wadanda EFCC ta kwato sun yi batan dabo a CBN
- Duk da sanarwar da ake ta yi tare da yada cewa an samo wasu kudade, babban bankin Najeriya, CBN ya kasa bayar da bayani kan kudaden
- Kungiyar kamfen tare da wayar da kai ta jam'iyyar All Progressives Congress, APC, cikin kwanakin nan ta ce an samo kudi har N1 tiriliyan na sata da kadarori cikin shekaru 6
- Sai dai kuma, babban bankin Najeriya ya kasa bayar da bayanin kudaden da aka samo tsakanin watan Janairun 2016 zuwa watan Disamban 2019
Babban bankin Najeriya ba shi da bayani ko daya kan kudaden da aka kwato na sata tsakanin watan Janairun 2016 zuwa watan Disamban 2019.
Ofishin audita janar na tarayya ya bayyana hakan a rahoton bayanan shige da ficen kudade da ya wallafa a shafin yanar gizo na 2019.
Wani bangare na rahoton ya ce:
Rahoton ya koka kan cewa, rashin fitar da bayanan kudin da aka kwato na sata zai iya janyo cece-kuce a cikin jama'a.
A sakamakon hakan, ofishin audita janar na tarayya ya bukaci gwamnan babban bankin Najeriyan da yayi bayani kan dalilin da yasa babu bayanan ko kuma su fuskanci hukuncin da ya dace.
A martani kan wannan zargin, babban bankin Najeriya ya ce babu wani kudi da aka samu tsakanin watan Janairun 2016 zuwa watan Disamban 2019 mai alaka da hakan.
Sai dai binciken da Legit.n gta gudanar ya nuna cewa, mulkin nan a tsakanin shekarun uku ya bayyana cewa an samo wasu kudaden sata da suka hada da na tsohon shugaban kasan mulkin soja, Janar Sani Abacha.
An karbo miliyoyin daloli daga Switzerland wadanda Abacha ya kai ya boye
A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta karbi $322.51 miliyan wanda Abacha ya handame daga Switzerland. Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta karbi dala miliyan 322.51 daga Gwamnatin Swiss daga cikin kudin da tsohon shugaban kasan, Gen. Sani Abacha ya handama.
Mai bada shawarar yada labarai ga Ministan kudi, Oluyinka Akintunde, yayi wannan jawabin jiya a Abuja. Akintunde yace babu wata cece kuce tattare da karbar kudin daga Gwamnatin Swiss.
Ministan kudin, Mrs kemi Adeosun, ta wanke kanta da hukumar kudi ta tarayya daga kudaden da Abacha ya handama.
Ministan bata taba rubuta wasika ga shugaban kasa ko wani daga cikin majalisar zababbu na tarayya (FEC) akan biyan lauyoyin da sukayi aikin karbo kudin.
Asali: Legit.ng