An karbo miliyoyin daloli daga Switzerland wadanda Abacha ya kai ya boye

An karbo miliyoyin daloli daga Switzerland wadanda Abacha ya kai ya boye

- Gwamnatin tarayya ta karbi $322.51 miliyan wanda Abacha ya handame daga Switzerland

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta karbi dala miliyan 322.51 daga Gwamnatin Swiss daga cikin kudin da tsohon shugaban kasan, Gen. Sani Abacha ya handama.

- Mai bada shawarar yada labarai ga Ministan kudi, Oluyinka Akintunde, yayi wannan jawabin jiya a Abuja. Akintunde yace babu wata cece kuce tattare da karbar kudin daga Gwamnatin Swiss

An karbo miliyoyin daloli daga Switzerland wadanda Abacha ya kai ya boye
An karbo miliyoyin daloli daga Switzerland wadanda Abacha ya kai ya boye

Gwamnatin tarayya ta karbi $322.51 miliyan wanda Abacha ya handame daga Switzerland. Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta karbi dala miliyan 322.51 daga Gwamnatin Swiss daga cikin kudin da tsohon shugaban kasan, Gen. Sani Abacha ya handama.

Mai bada shawarar yada labarai ga Ministan kudi, Oluyinka Akintunde, yayi wannan jawabin jiya a Abuja. Akintunde yace babu wata cece kuce tattare da karbar kudin daga Gwamnatin Swiss"Mministan kudin, Mrs kemi Adeosun, ta wanke kanta da hukumar kudi ta tarayya daga kudaden da Abacha ya handama.

"Ministan bata taba rubuta wasika ga shugaban kasa ko wani daga cikin majalisar zababbu na tarayya (FEC) akan biyan lauyoyin da sukayi aikin karbo kudin.

DUBA WANNAN: Jami'ar OAU ta yi bayani kan Farfesa dake raba maki dan lalata

Ta kara da cewa ba a samu wani matsala ba tattare da karbar kudin. "mun fada cewa dala miliyan 322,515,931.83 sun shigo cikin wani asusu na musamman na babban bankin Najeriya (CBN) a ranar 18 ga disamba, 2017 daga Gwamnatin Swiss.

Kamar yanda Akintunde ya fadi, ministan ta qalubalanci biyan dala miliyan 16.9 ga lauyoyi biyo da suka karbo kudin da aka handame.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng