Matashi zai auri mata biyu rana guda bayan ya dirka musu ciki
- Mutane a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan sabuwar katin gayyatar aure a jihar Delta
- Wani Mutumi mai suna John Erere Nana na gab da angwancewa da mata biyu bayan dirka musu juna biyu
- Auren wanda aka shirya ranar Asabar na shan yabo da suka bakin jama'a
Ughelli, Delta - Wani mutumi dan jihar Delta, kudancin Najeriya na gab da angwancewa da dirka-dirkan mata biyu lokaci guda.
Mutumin mai suna John Erere Nana zai auri yan matan masu suna Patience Boyi da Elohor Dudu ne bayan sun dauki juna biyu daga garesa.

Asali: Facebook
A hotunan da Instablog9ja ya daura kan Instagram, an shirya auren gargajiyan ne a makarantar Firamaren Ishere dake Oviri Agbarho, karamar hukumar Ughelli North, jihar Delta.

Kara karanta wannan
Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau
Dukkansu yan jihar Delta, sun sanya irin kaya guda a hoton dake jikin katin gayyatan.
Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu:
Comrade S.N yace:
Kai wannan ba karamin jarumi bane gaskiya ..
Bana shi zamu bawa kyautar Gwarzon Shekara a bisa wanga kokari da yayi✌
Khalid Hassan Abubakar:
Wannan shege ne, Shegantaka se Anna
Muktar Mahmud Muktar:
Lalle yayi kokari sosai
Saifullahi Sa'idu Gangara
Da an Bari sun haihu a had'a da Suna kawai
Aleeyou Habeeb Abdoulkhareem:
gwaji yayi kuma yanzu ya tabbatar da cewa ba juyoyi ze auro
Asali: Legit.ng