Yadda masu garkuwa da mutane suka bi mata da miji gona suka sace su
- ‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aurata, London da matarsa Blessing Omoru a gonarsu da ke kauye a karamar hukumar Obokun cikin jihar Osun
- An samu bayanai akan yadda su na gonarsu da ke kauyen Ori-Omipupa ta wuraren Agric suka ji ‘yan bindiga sun isa da misalin 9pm su na harbe-harbe
- Sai dai wasu jami’an tsaro bayan samun rahoton sun bi sawun su amma ba su samu nasarar ceto su ba saboda ‘yan bindigan sun bayyana ne da miyagun makamai
Jihar Osun - ‘Yan bindiga sun sace wani magidanci, London da matarsa, Blessing Omoru a cikin gonarsu da ke wani kauye a karamar hukumar Obokun a cikin jihar.
The Nation ta tattaro bayanai akan yadda miji da matar suke cikin gonarsu da ke kauyen Ori-Omipupa kusa da wuraren Agric, ‘yan bindigan sun yi dirar mikiya su ka hau harbe-harbe da misalin 9pm.
Wani mazaunin kauyen ya tabbatar da harin
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa The Nation cewa:
“Yan bindiga sun shiga wuraren gonar inda su ka dinga harbe-harbe, ana wannan yanayin ne su ka yi garkuwa da mutanen.
“Masu gadin gargajiya da ake kira Kiriji Heritage Defenders sun samu labari akan harin, shugabansu Ademola Ekundayo tare da yaransa sun bi sawun ‘yan bindigan amma abin ya ci tura don sun je da miyagun makamai ne.
“Daga baya muka sanar da ‘yan sanda wadanda har yanzu ba su samu sun ceto su ba. Yaran Kiriji su na daji tare da ‘yan sanda.”
Wata majiya daga jami’an tsaro ta sanar da yadda ‘yan bindigan su ka sace miji da matar da niyyar samun kuadaden fansa daga jama’an garin saboda lamarin ya auku ne tsakanin Esa-Oka da Esa-Odo.
Har yanzu ana ci gaba da kokarin ceto su
Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, SP Yemisi Opalola ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Kamar yadda ta ce, da misalin karfe 10:45pm wani Moses Imomiuku na titin Ayetoro ya kai rahoto ofishin ‘yan sandan Esa Oke cewa da misalin karfe 10pm wani Andrew Omoru ya sanar da shi cewa an sace iyayensa a gonarsu.
Kakakin ta ce lokacin da jami’an rundunar ‘yan sandan suka isa wurin sun daura aniyar hada kai da ‘yan sa kai na OPC don ceto wadanda aka sace.
Yayin hakan ne tace sun samu nasarar ceto babur din wadanda aka sata sannan har yanzu su na ci gaba da kokartawa.
Asali: Legit.ng