Siyasar Kano: Yan sanda sun damke mutum 13 da hannu a ƙone ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau

Siyasar Kano: Yan sanda sun damke mutum 13 da hannu a ƙone ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau

  • Hukumar yan sanda reshen Kano ta tabbatar da cewa ta shawo kan halin da aka shiga bayan harin yan daba a Ofishin APC
  • Kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace jami'an da hukumar ta tura sun cafke mutum 13 tare da kwato wasu makamai
  • Yace hukumar yan sanda zata cigaba da bincike kan masu hannu a harin, kuma zasu fuskanci hukunci

Kano - Hukumar yan sanda reahen jihar Kano, ranar Alhamis, tace ta damke mutum 13 dake da hannu a kone ofishin yakin neman zaɓen gwamna na Sanata Barau Jibrin.

Tribune Online ta rahoto cewa wasu yan daba sun kona ofishin, wanda ke a kan hanyar Maiduguri a cikin birnin Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa yan daban suna ɗauke da makamai masu hatsari, wanda ya tilasta wa mutanen yankin nesa da su kada abin ya shafe su.

Kara karanta wannan

Labari cikin Hotuna: Yadda Yan daba suka kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau a Kano

Jam'iyyar APC
Siyasar Kano: Yan sanda sun damke mutum 13 da hannu a ƙone ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekaru Hoto: Musbahu Rabiu Gyadi-Gyadi
Asali: Facebook

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yau 2 ga watan Nuwamba, 2021 da misalin karfe 8:00 na safe, mun samu rahoton cewa wasu yan daba sun kai hari tare da lalata Ofishin Sanata Barau Jibrin mai wakiltar arewacin Kano, wanda ke kan hanyar Maiduguri."
"Bayan samun wannan rahoton, nan take kwamishinan yan sanda, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko, ya umarci jami'an Operation Puff Ander su mamaye wurin, kuma su shawo kan lamarin."
"Nan take jami'an suka cika umarni, suka dira wurin kuma suka cafke yan daba 13, bayan haka kuma suka kwace makamai masu hatsari 34, da sanduna 23 da jarkokin fetur."

Wane hali ake ciki yanzun?

Kakakin yan sanda ya tabbatar da cewa a halin yanzun jami'ai sun dawo da zaman lafiya kuma komai ya koma karkashin ikon su a ofishin, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano

Bugu da kari yace ana cigaba da bincike kan abinda ya faru, kuma waɗan da suka shiga hannu zasu gurfana gaban kotu domin su girbi abinda suka shuka.

A wani labarin na daban kuma Malami ya bayyana dalilan da yasa gwamnatin tarayya ta ki fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci

Wannan na zuwa ne duk da matsin lamba da kiraye-kiraye da ake wa shugaban kasa Buhari daga kowane ɓangare kan ya bayyana sunayen mutanen dake ɗaukar nauyin ta'addanci.

Ministan ya tabbatar da cewa sunayen dake hannunsu ya kunshi yan cikin kasa da kuma sanannu da aka sani a kasashen duniya kuma suna da hannu a ayyukan ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262