Sojoji sun sheke dan IPOB yayin da tsagerun ke kokarin sace likitoci a jihar Imo
- 'Yan ta'addan IPOB sun hadu da fushin hukuma yayin da suke kokarin yin awon gaba da wasu ma'aikatan kiwon lafiya
- A rahoton da muke samu daga majiya, an ce an hallaka daya daga cikin 'yan IPOB din, yayin da aka kame mutum daya
- Rundunar soji ta ceto ma'aikatan kiwon lafiyan, inda ta mika su ga wani wuri mai aminci a jihar Imo
Imo - Dakarun rundunar soji ta “Exercise Golden Dawn Sector 3” sun yi nasarar kashe wani dan haramtacciyar kungiyar IPOB/ESN a wani artabu da suka yi a karamar hukumar Amauju Isu ta jihar Imo, Leadership ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar, ya ce ‘yan IPOB sun yi yunkurin yin garkuwa da wasu likitoci da ma’aikatan jinya na kungiyar “Doctors on the move Africa”.
Ya ce ma’aikatan jinyan na kan aikin ba da kulawar lafiya kyauta ga mazauna unguwar Amucha da ke karamar hukumar Njaba ta jihar Imo ne lokacin da kungiyar IPOB/ESN ta far musu.
A cewarsa:
“Rundunar sojojin tare da rundunar sojojin saman Najeriya ta 211 Quick Response Group da kuma ‘yan sandan Najeriya bisa samun bayanan sirri kan shirin aikata laifin, cikin gaggawa suka shiga suka ceto tawagar likitocin.
“An raka tawagar likitocin zuwa wani wuri mai aminci. Bayan haka ne sojojin suka bi bayan ‘yan ta’addan tare da gano su a karamar hukumar Amauju Isu ta jihar Imo, inda aka same su suna aiwatar da dokar zaman gida a Amauju.
“A musayar wutan da ya barke, an kashe daya daga cikin masu laifin, yayin da sauran suka tsere."
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daya daga cikin 'yan ta'addan da ya tsira da harbin bindiga shi ma ya shiga hannun hukuma yayin da 'yan banga suka kamo shi.
A cewar Nwachukwu:
“Daya daga cikin su, wanda ya tsere da harbin bindiga, daga baya jami’an ‘yan banga sun kame shi, suka mika shi ga ‘yan sanda.
"Rundunar sojojin sun kwato bindigar famfo guda daya, harsashi guda biyar, mota Lexus 300 XR SUV daya da wayar hannu."
FG ta zargi ESN da yanka wasu ‘yan sanda tare da yada bidiyon gawarwakinsu a intanet
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta zargi kungiyar tsaro mai alaka da IPOB ta Eastern Security Network (ESN) da kashe ‘yan sanda biyu a jihar Anambra.
Zargin na kunshe ne a wata sanarwa da ministan yada labarai da al’adu na Najeriya, Lai Mohammed ya aikewa majiyar Legit.ng a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba.
Gwamnati ta yi gargadin cewa za a kama wadanda suka aikata kisan, suka dauki hoton danyen aikin da suka aikata, suka yada irin wannan abu, kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Asali: Legit.ng