Dubun wasu gawurtattun masu garkuwa 32 ya cika, yan sanda sun kwato muggan makamai
- Jami'an yan sanda sun samu nasarar kame wasu mutum 32 da ake zargi da aikata garkuwa da kuma satar shanu
- Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin su akwai gawurtattun masu garkuwa da suka shiga hannu a yankin arewa ta yamma
- Haka nan kuma yan sanda sun kwato makamai da dama da suka haɗa da bindigun AK-47 da alburusai
Abuja - Rundunar yan sandan ƙasar nan (NPF) ta damke wasu gawurtattun masu aikata manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa, ayyukan yan bindiga da sauran su.
Leadership tace kakakin yan sanda na ƙasa, Frank Mba, ya bayyana cewa an damke waɗan da ake zargin ne bayan samun wasu bayanan sirri.
Yace jami'ai sun samu nasarar cafke wasu daga cikin su ne a samamen da suka kai yankin Arewa ta yamma da ya haɗa da jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna, Kebbi da kuma Neja.
Jami'an sun kwato muggan makamai daga hannun mutanen, AK-47 guda 19,, ƙaramar bindigar hannu uku, Machine Gun guda ɗaya, da kuma wukake.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mba ya kara da cewa jami'an sun kuma samu nasarar kwato alburusai 453 da kuma motoci ƙira daban-daban guda 17.
Daga cikin mutanen da suka shiga hannu akwai, Salihu Ibrahim, Aliyu Suleiman, da kuma Abdullahi Suleiman, waɗan da suka sace makotan su mata hudu.
Yadda suka yi garkuwa da mata 4
A cewar ɗaya daga cikin waɗan da ake zargin, Salihu Ibrahim, ya haɗa baki da sauran mutum biyu suka sace mata 4, cikin su harda mai juna biyu.
Yace kwata-kwata ba su da sa'a yayin da jami'an yan sanda suka bibiye su, suka kame su, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Daya daga cikin mutanen da suka faɗa sharrin masu garkuwan, Abdul Bature, yace maharan suna yi masa aiki ne, kuma sun sace masa shanu 30 tare da jikkata wasu.
Ya roki jami'an yan sanda su ɗauki mataki mai tsauri kan mutanen domin ya zama izina ga sauran masu aikata makamancin irin haka.
A wani labarin na daban kuma yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda cewa su gaggauwa kawo miliyan N200m kafin su bar wurin sabis
Yan bindigan da suka sace matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun nemi iyalan wani ɗan sanda su biya fansa.
Rahoto ya bayyana cewa maharan sun nemi a tattara musu miliyan N200 cikin awanni 6 kafin su bar gurin sabis.
Asali: Legit.ng