BaAmurkiya mai digiri 4 ta gangaro Afrika, ta yi wuff da dan achaba, tace hadin Ubangiji ne
- Wata baAmurkiya mai suna Carey Joy, ta auri mijin ta mai suna Albert Wanyonyi dan asalin kasar Kenya daga Bungoma a 2018
- Carey wacce ta je a matsayin mishan kasar, ta ce Ubangiji ne ya bayyana mata cewa dan achaban ne mijinta yayin da suka hadu
- Abinda ya bai wa jama'a masu yawa mamaki shi ne yadda suke da banbanci a fannin ilimi, ta na da digiri hudu yayin da mijin nata ya bar makaranta a aji 2 na firamare
Carey Joy da Albert Wanyonyi bayani ne gamsasshe kan cewa soyayya ruwan zuma ce.
Carey wacce ta je mishan kasar Kenya ta aure Wayonyi, wanda da kyar ya ke iya bayani da turanci tunda a makarantar firamare ya tsaya da karatu.
A tattaunawar da aka yi da shi a bayan, Wayonyi ya ce ya fada kaunar matarsa duk da cewa akwai kalubale da banbancin da suke da shi na yare.
Carey ta na da digiri hudu
A yayin jawabi yayin da gidan talabijin din TV 47, mahaifiyar kyawawan yara biyun ta bayyana cewa ta na da digiri hudu a fannoni daban-daban. Daya daga ciki na tattalin arziki ne.
Carey ta yi bayanin cewa Ubangiji ne ya sanar da ita ce Wanyonyi ne zababben mijin ta yayin da ya gabatar da kan shi gare ta, hakan yasa ba ta damu ba duk da bashi da ilimi.
"A yayin da ya ke gabatar da kansa gare ni, Ubangiji ya yi min magana kuma ya ce shi ne miji na kuma ba zan taba samun wani ba idan na koma gida," tace.
Baturiyar ta ce ta na jin dadin zama da mijin ta a kauyensu mai suna Bungoma. Ta kara da cewa, kafin ta koya yaren Swahili, suna magana ne ta hanyar fahimta da kuma alamu.
Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi
A wani labari na daban, Wani mutumin kirki mai suna Ajay Munot ya bai wa diyarsa kyauta wacce ba a taba bayarwa ba a matsayin kyautar aure. Ya ginawa talakawa gidaje casa'in domin shagalin bikin diyar shi inda ya bayar da su kyauta domin karrama ta.
Kafin wannan ranar, mutumin ya kwashe shekaru yana tara kudin shagalin bikin. Amma da lokaci yayi kuma ya ga jama'ar yankin suna fama da talauci, sai ya fada damuwa kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.
Da yawan kudin da ya adana domin bikin diyar shi, mutumin ya yi tunanin cewa zai iya amfani da kudin wurin ginawa jama'a gidaje masu kyau.
Asali: Legit.ng