Cikin kwana 30 zamu dawo da wutar lantarki zuwa gidajen mutane a Maiduguri, Gwamna Zulum

Cikin kwana 30 zamu dawo da wutar lantarki zuwa gidajen mutane a Maiduguri, Gwamna Zulum

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno, ya sha alawashin yin duk me yuwu wa wajen dawo da hasken wutar lantarki Maiduguri
  • Zulum ya bayyana cewa idan Allah ya yarda nan da kwana 30 kacal wuta zata koma kamar da a babban birnin da kewayensa
  • Maiduguri ta shafe dogon lokaci babu wuta, tun bayan da yan ta'adda suka lalata tashar wutan watanni 11 kenan da suka wuce

Maiduguri, Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya sha alwashin maida wutar lantarki a Maiduguri da kewayenta cikin kwana 30, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Babban birnin jihar Borno ya shiga cikin halin rashin wuta tun sanda yan ta'adda suka lalata tashar rabon wutar lantarkin dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, watanni 11 da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

Gwamna Zulum
Cikin kwana 30 zamu dawo da wutar lantarki zuwa gidajen mutane a Maiduguri, Gwamna Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 a gaban majalisar dokokin jihar, ranar Talata, Gwamnan yace aiki ya yi nisa wajen tabbatar da lantarki ta dawo.

Gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan Allah (SWA) ya yarda zamu nunka kokarin da muke wajen tabbatar da hasken wutar lantarki ya dawo Maiduguri da kewaye cikin kwanaki 30."
"Kamar yadda kuka sani babban birnin mu ya rasa wutar lantarki kimanin shekara ɗaya kenan da ta shuɗe. Ba zamuyi ƙasa a guiwa ba ta ɓangaren mu, har sai komai ya dai-daita."

Meyasa tun baya ba'a gyara ba?

Gwamnati ta yi kokarin gyara wutar a lokuta da dama da suka shuɗe amma sai yan ta'adda su sake maida hannun agogo baya.

Rashin wutar lantarki ya cigaba da durkusad da mazauna yankin, da kasuwancin su, da kuma hukumomin gwamnati waɗan da aikinsu ya dogara da wuta.

Kara karanta wannan

'Kada ku mayar da Jigawa kamar Spain', Gwamna Badaru ya yi barazanar dawo da kullen korona

Jami'ar Maiduguri (UNIMAID) ta bayyana cewa tana kashe kimanin miliyan N10m duk wata wajen samar da wuta daga janareto, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Kungiyar kiristoci CAN ta maida martani kan rage ranaƙun aiki da gwamna El-Rufa'i ya yi a jihar Kaduna

Kungiyar kiristoci CAN ta shawarci ma'aikatan jihar Kaduna su daina murna da matakin rage ranakun aiki da gwamnatin jiha ta ɗauka.

CAN tace kamata ya yi su dage da addu'a kada gwamnatin ta rage musu albashi, ko ta sake sallamar wasu daga aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262