Rashin Adalci Ne Musulmi Ya Zama Shugaban Ƙasa Bayan Buhari, Ƙungiyar Kirista, PFN

Rashin Adalci Ne Musulmi Ya Zama Shugaban Ƙasa Bayan Buhari, Ƙungiyar Kirista, PFN

  • Shugaban kungiyar kirista ta PFN, Bishop Francis Oke ya ce ba adalci bane wani musulmi ya zama shugaban kasa bayan Buhari
  • Babban malamin addinin kiristan ya bayyana hakan ne bayan taron da kungiyar ta PFN ta yi a Legas
  • Bishop Oke ya ce idan aka lura tun bayan dawowa mulkin demokradiyya a 1999, karba-karba ake yi tsakanin musulmi da kirista

Kungiyar Kirista ta Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta bukaci cewa kirista ne ya dace ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023, tana mai cewa rashin adalci ne wani musulmi ya sake zama shugaba.

Shugaban PFN na kasa, Bishop Francis Wale-Oke, ne ya yi wannan kiran a karshen taron kungiyar da aka saba yi duk bayan wata hudu, da wannan karon aka yi a Legas.

Rashin Adalci Ne Musulmi Ya Zama Shugaban Ƙasa Bayan Buhari, Ƙungiyar Kirista, PFN
Ba adalci bane musulmi ya gaji Buhari, Shugaban PFN. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

An gano abin da Buhari ya fadawa Shugaban kasar Afrika ta Kudu kafin ya lula zuwa Dubai

This Day ta rahoto shugaban na PFN na cewa:

"Ba mu tunanin ya dace wani musulmi ya sake zama shugaban kasa a 2023. Zuwa 2023, musulmi ya yi mulki na shekara takwas. Coci ta mara masa baya. Mun masa addu'a kuma mun bashi goyon baya. Ba mu yi nadama ba. Amma yanzu shugaban kasa kirista muke so."

Ya kara da cewa idan aka yi nazarin yadda shugabancin kasar ke tafiya, karba-karba ake yi tsakanin musulmi da kirista tun shekarar 1999, Obasanjo, Yaradua, Jonathan sai Buhari.

"Bai dace daga Shugaba Buhari sai wani musulmin ba. Wannan ba zai adalcu ba. Ya kamata mu yi abin da ya ke dai-dai. Ubangiji mai son adalci ne."

Shugaban PFN ya yi magana kan talauci da balaguro da yan Nigeria ke yi zuwa kasar waje

Kara karanta wannan

Buhari zai gyara Najeriya tsaf kafin ya sauka a mulki a zaben 2023, inji Sanata

Shugaban na PFN ya kuma jadada kirar da kungiyar ta yi wa gwamnatin tarayya ta kira taro don tattaunawa kan manyan abubuwa biyu da ke adabar kasar da ke cigaba da jan yajin aiki da saka matasa barin kasar.

Malamin ya ce:

"Ya kamata shugabannin mu su sake dagewa. Muna godiya bisa aikin da suke yi amma ya kamata su kara kaimi. Darajar naira a kasuwar duniya abin damuwa ne kuma ba mu amince da shi ba.
"A dauki mataki game da tattalin arzikin kasar. Wahalar ya yi yawa. Mutane na fama da yunwa. Ya kamata mu yi wani abu. Allah ya taimake mu."

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

A wani labarin daban, Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, a Jos, babban birnin jihar Plateau ta roki shugabannin musulmi da na kirista su dena tunzura mutane suna miyagun ayyuka, Peoples Gazette ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya zaman makoki a kasar na daf da zuwa karshe

A cewar sanarwar da ta fitar a garin Jos a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugaban CAN, Polycarp Gana da satare Ezekiel Noam, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Yalwan Zangam.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka garin a daren ranar Talata sun kashe mutane masu yawa sannan suka kona gidaje da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164