Matashi ya ziyarci birnin zinari inda mutane ke wanke fuska da shi, bidiyo da hotunan sun gigita jama'a
- Wani mai yawon bude ido, Joe Hattab, ya shayar da ma’abota amfani da kafafen sada zumunta mamaki bayan ya wallafa bidiyonsa a wani fitaccen gari da ke kasar Japan
- A cikin garin akwai zinare mai tarin yawa wanda su suke sayar wa da kusan yawancin kasashen da ke nahiyar Asia zinaren saboda tsabar yawansa a garin
- Joe ya wanke fuskarsa da zinare maimakon ruwa kuma ya sha shayin zinare, har ila yau ya nuna yadda zinare ya ke lullube da alawa mai kankara ta Ice Cream
Yayin da wasu suke ganin zinare a matsayin ma’adani mai kimar gaske da tsada, garin Kanazawa ba su dauke shi a matsayin wani kayan gabas ba.
Wani mai yawon bude idanu, Joe Hattab ya ya gano hakan bayan ya kai ziyara wani gari da ke Japan.
Joe, a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, ya nuna wasu yankuna da ke cikin kasar mai arziki da mutanen ta.
Su na zuba zinare a kusan komai
Mutanen Kanazawa su na da arzikin zinare saboda haka suke sa shi a cikin komai. Garin ne ke samar da fiye da kaso 90% na zinare ga kasar Japan, har sa shi suke yi cikin alawa mai kankara ta Ice Cream.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Joe ya yi mamaki akan yadda mutanen garin suke shan Ice Cream da shayi wanda akwai zinare a cikinsa inda ya ce yana ganin akwai wata alfanu tattare da shi.
Wani ma’aikacin gidan abinci wanda ya mika wa mai yawon bude idon Ice Cream mai zinare ya bayyana cewa, akwai yuwuwar kamuwa da cuta ta kaso 0.0001% idan mutum ya ci abu mai dauke da zinare a cikinsa. Duk da dai zinaren ba ya da dandano.
Bidiyon wani mai yawon bude ido a garin da mutane ke wanke fuskokinsu da zinare ya karade kafafen sada zumunta
Nan da nan jama’a su ka fara cece-kuce a karkashin bidiyon inda wata Aamie Xierah ta ce:
“Zinare zai iya cutar da lafiyar ka. Ko kuwa?.. Ko da yake, kusan komai yana cutar da lafiya har ganyayyaki da ‘ya’yan itace su na da sinadarai a cikinsu.”
Sami Redcliffe ya ce:
“Wannan lamari da ban dariya yake. Ta ya za a yi mutum ya ci zinare, anya ba ya da illa a jikin mutum? Maimakon ciyar da yaran talakawa da suke yunkurin mutuwa da yunwa ku na nan ku na kashin zinare. Zaku iya amfani da shi ku gina wa talakawa gidaje.”
Shailendra Patil ta ce:
“Zinare na da amfani ga lafiyar mutum, idan ka ga magungunan indiyawa za ka gane akwai zinare ko kuma azurfa amma mara yawa don amfanar da lafiya.”
Khalid Hassan Raza ya ce:
“Burin mutum ba ya taba karewa in har bai dakatar da zuciyarsa daga bukatu ba. Maimakon kashin zinare, ga talakawa can su na fama da abinda za su ci cike da kunci.”
Bidiyon yaron da ya ɓoye cikin injin jirgin sama don tsananin son zuwa ƙasar waje, ƴan sanda sun kama shi
Asali: Legit.ng