Jami'an NDLEA sun yi ram da tsohuwa mai shekaru 70 dauke da miyagun kwayoyi
- Jami'an hukumar NDLEA sun kama wata tsohuwa mai suna Beatrice Aigbedion mai shekaru 70 da 5,000kg na miyagun kwayoyi a jihar Edo
- Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun makamai (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama tsohuwar tare da wasu dillalan miyagun kwayoyi masu yawa
- Har ila yau, jami’an NDLEA sun je wata ma’ajiyar kaya a Uhiere cikin jihar inda suka samu wiwi mai nauyin 4,261.5kg
Jami’an hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi sun yi ram da wata tsohuwa mai suna Beatrice Aigbedion mai shekaru 70 da wasu miyagun kwayoyi fiye da nauyi 5,000kg a jihar Edo.
Hukumar NDLEA din ce ta bayyana hakan ta wata takarda ta ranar Lahadi, inda ta ce jami’an sun kama wacce ake zargin da wasu da dama a cikin jihar, Channelstv ta ruwaito.
“Bayan kwanaki jami’an NDLEA suna bincike, sun afka wata ma’ajiya da ke Uhiere, karamar hukumar Ovia ta arewa maso gabas da ke jihar, inda suka samu wiwi 4,261.5kg sannan suka kama wani da ake zargi, Ikong Stanley.
“Yayin da aka kama ta a Irrua ranar Larabar da ta gabata, Mrs Aigbedion mai shekaru 70 da magungunan tari kamar Codeine, Swinol da Rohypnol tare da wata mai sayar da kayan maye, Joseph Onyemaechi mai shekaru 50 a Ikpoba Okha, a Sakponba-Benin City a ranar Juma’a da kayan maye iri-iri mai nauyi 2.055kg.
"Sannan sun kama Gabriel Akioya da Isa Salihu a ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamba a Irrua, karamar hukumar Esan ta tsakiya da magungunan tari kamar Codeine, Tramadol, Swinol da Rohypnol.”
Har ila yau, jami’an NDLEA a cikin ranakun karshen mako sun kama 12,385kg na wasu miyagun makamai ciki har da wiwi wanda aka shigo dasu daga kasar ketare ta jihar Legas ta ruwa.
Sannan masu binciken sirri sun gano yadda aka shigo da wasu miyagun kwayoyi guda 12,385 jihar Legas daga wata kasa ta Afirka ta yamma ta ruwa.
An samu bayanai akan yadda jami’an tsaro na ruwa a ranar Asabar 27 ga watan Nuwamba suka kwace miyagun kwayoyi cikin manyan motoci biyu da kuma wata mota kirar Sienna.
Channelstv ta ruwaito cewa, yayin wani sintiri, jami'an sun kama wasu mutane 3, Abdulkadri Zakari, Ka’abu Sausu da Lawrence Adie.
A jihar Delta, jami’an hukumar sun afka Hampton Towers da Spa Hotel, titin Okpanam, Asaba inda aka kama Thompson Chukwemeka da Dobedient Etumudor da miyagun kwayoyi iri-iri.
Har ila yai a jihar Kano, jami'ai sun kama Alhaji Bukar Malan Abdu da 143kg na miyagun kwayoyi daga hannunsa sannan aka kama 466kg na kwayoyin caga wani Bashir Shuaibu dan asalin jihar Edo amma yake harkar wiwi a Kano.
Jami'an kwastam sun kwace tirela 12 ta shinkafa da miyagun kwayoyi a Ogun
A wani labari na daban, jami'an hukumar kwastam ta kasa, reshen jihar Ogun ta kama buhu 7,311 na shinkafar gwamnati wacce aka loda a tireloli 12 a jihar. Har ila yau, ta kama fakiti 124 da sunki 164 na wiwi mai nauyin 167kg, Punch ta ruwaito.
Shugaban hukumar na yankin, Dera Nnadi, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawa da manema labarai a ofishin NCS da ke Abeokuta, babban birnin jihar.
Shugaban ya bayyana cewa, hukumar ta cafke wasu mutum biyu wadanda ke kokarin kai kwayoyi Ijebu-Ode da ke kan hanyar kudu maso gabas.
Asali: Legit.ng