Innalillahi: Fitaccen dan kasuwa, Alhaji Sani Buhari, ya riga mu gidan gaskiya
- A sanyin safiyar yau ne hamshakin attahijiri kuma dan kasuwa, Alhaji Sani Buhari ya riga mu gidan gaskiya
- Rahotanni da muke samu sun shaida cewa, hamshakin dan kasuwan ya rasu ne yau Lahadi a daular larabawa; Dubai
- Alhaji Sani Buhari, hamshakin dan kasuwa ne, wanda ya kirkiri kamfanin Standard Construction Limited da sauransu
Dubai - Hamshaki kuma gawurtaccen dan kasuwa Alhaji Sani Buhari Daura ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta ruwaito.
Rahoto daga majiya ya tattaro cewa hamshakin dan kasuwar ya rasu ne a Dubai da sanyin safiyar yau Lahadi.
Ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.
An haifi fitaccen dan kasuwan ne a garin Daura na jihar Katsina a watan Janairun 1932.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har zuwa rasuwarsa, shi ne mamallakin Kamfanin Standard Construction Limited kuma Shugaban Kamfanin Bayajida Group.
Ya yi karatun Islamiyya a karkashin mahaifinsa, wanda shi ne Khadi na Daura, daga baya kuma ya koma Daura Elementary School a 1938.
Ya bude kamfanin Bayajida Amenity Trading Company, kamfaninsa na farko kenan a jihar Kano a shekarar 1962.
Bayan shekaru takwas, kamfanin ya canza suna zuwa Bayajida Nigeria Limited.
An karrama shi da lambar hidima ga kasa na OON a shekarar 2003.
Ya fito ne daga mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda Pulse ta ruwaito.
Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya
A wani labarin, tsohon dan takarar gwamna a jihar Ekiti, Sanata Gbenga Aluko ya rasu. An ce dan siyasar haifaffen Ode-Ekiti ya rasu ne a ranar Asabar bayan da ya fadi a ofishinsa da ke Abuja, Punch ta ruwaito.
A cewar Continental Television, an garzaya da shi asibiti inda ya rasu. TVC ta ruwaito cewa daya daga cikin hadiman Aluko da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa Aluko lafiyarsa lau, amma haka dai ya rasu.
Wata majiya ta bayyana cewa marigayin dan siyasar ya rasu ne sakamakon bugun zuciya. Ya kasance da ne ga marigayi masanin tattalin arziki, Farfesa Sam Aluko.
Asali: Legit.ng