Tinubu ya kawo min ziyara kan maganar takararsa a zaben 2023, Alhaji Tanko Yakassai

Tinubu ya kawo min ziyara kan maganar takararsa a zaben 2023, Alhaji Tanko Yakassai

  • Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa ya karbi bakuncin Jagoran jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu
  • Dattijon ya bayyanawa yan Najeriya cewa sun tattauna ne kan maganar takarar Tinubu kujerar shugaban kasa
  • Bola Ahmed Tinubu ya yi wannan ganawar ne da Alhaji Yakassai a gidansa dake birnin tarayya Abuja

Abuja - Daya daga cikin dattawan Najeriya masu sharhi kan lamuran yau da kullum, Alhaji Tanko Yakassai, ya bayyana abinda ya tattauna da Asiwaju Bola Tinubu lokacin da ya kai masa ziyara.

Tinubu, wanda ake kyautata zaton cewa zai yi takara a zaben shugabancin kasa a 2023 ya ziyarci Alhaji Tanko Yakassai a gidansa dake Abuja ranar Laraba, 23 ga Nuwamba, 2021.

Yayin hira da Jaridar Punch ranar Juma'a, Alhaji Yakassai ya bayyana cewa Tinubu ya kawo masa ziyara ne don neman goyon bayansa a takarar zaben 2023 da yake niyyar yi.

Kara karanta wannan

'Yan APC a Arewa sun fara gangamin nuna goyon baya ga Okorocha ya zama shugaba a 2023

Tinubu da Alhaji Tanko Yakassai
Tinubu ya kawo min ziyara kan maganar takararsa a zaben 2023, Alhaji Tanko Yakassai Hoto: Festus Olanrewaju Ojo
Asali: Facebook

Dattijon, wanda ke da shekaru 96 ya bayyana cewa lallai zai goyi bayan Tinubu a zaben 2023.

A cewarsa:

"Ya zo ziyara na amma ina da yan takara biyu da nike da niyya a zuciyata dama da nace wanda ya fara neman goyan baya na, shin zan goyi baya. Tinubu ne na farko."

Yakassai ya bayyana cewa Tinubu ya laburta masa niyyar takara a zaben shugaban kasa.

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bukaci 'yan Najeriya da su saurara har zuwa watan Janairu 2022 domin jin ta bakin jagoran jam'iyyar All Progressives Congress na kasa, Bola Tinubu, kan ko zai yi takarar shugaban kasa a 2023 ko a'a.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ga PDP: Ku bar tikitin shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo

Fashola ya bayyana hakan ne a wani shirin Channels TV a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba.

A yan baya-bayan nan, an gano fastocin Tinubu inda ake rade-radin yana neman takarar kujerar shugaban kasa a manyan birane ciki harda Lagas da Abuja.

Koda dai Tinubu bai fito ya ayyana aniyarsa na takarar kujerar ba a 2023, akwai rahotanni da alamu da ke nuna cewa watakila yana da ra'ayin neman kujerar ta daya a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng