Ya kamata a bari yan Najeriya su mallaki bindigogi na kansu, Gwamna Masari
- Da yiwuwan yan Najeriya su fara mallakar bindigogin kansu don kare kawunansu daga ta'addancin yan bindiga
- Gwamnan jihar Katsina ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta baiwa yan Najeriya damar mallakar bindiga
- Masari ya bayyana hakan ne yayinda ya kai ziyara ga Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ranar Laraba, ya yi kira ga Gwamnatin tarayya ta baiwa yan Najerya daman mallakar bindigogi don kare kansu daga yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Tribune ta ruwaito Masari na cewa ba zai yiwu a zuba ido wadannan yan bindiga su cigaba da kashe mutane a fadin tarayya ba.
Ya yi wannan magana ne lokacin da ya kai ziyara ga Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, don jajanta masa bisa kisan matafiya a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A riwayar Thisday, Gwamna Masari yace ya kamata a fahimci babu ruwan addini da kabilanci da matsalar tsaro.
"Ya kamata mu fitar da sabuwar hanyar maganin wadannan mutanen saboda dabbobi ne kawai masu addabar mutane," yace.
Asali: Legit.ng