Kano: 'Yan kasuwa sun koka kan jagoranci rushe shaguna da shugaban KAROTA yayi a kasuwar waya

Kano: 'Yan kasuwa sun koka kan jagoranci rushe shaguna da shugaban KAROTA yayi a kasuwar waya

  • 'Yan kasuwa masu tarin yawa da ke sana'ar siyar da wayoyi da kayayyakinsu a Farm Centre da ke Kano sun shiga tashin hankali sakamakon asarar da suka tafka
  • 'Yan kasuwan sun bayyana yadda shugaban KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi ya jagoranci rushe musu shagunansu duk da kuwa akwai kayan miliyoyi a ciki
  • A cewar 'yan kasuwan, sun yi taro da Dan Agundi da dare inda yace su kwashe kayansu nan da kwana biyu, amma sai rusau suka gani da safe
  • Sai dai Dan Agundi ya musanta inda yace an basu notis na wata daya amma suka yi kunnen uwar shegu da hakan, shiyasa suka dauka matakin nan

Kano - 'Yan kasuwa masu tarin yawa da ke da shaguna a kasuwar waya ta Farm Centre a Kano sun koma zauna gari banza sakamakon asarar da suka tafka bayan shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi ya jagoranci jami'ansa wurin rushe shagunansu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagun suka kai Plateau

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan ne karo da biyu da shugaban hukumar KAROTA ya jagoranci rushe shagunan jama'a a cikin sati daya.

Kano: 'Yan kasuwa sun koka kan jagoranci rushe shaguna da shugaban KAROTA yayi a kasuwar waya
Kano: 'Yan kasuwa sun koka kan jagoranci rushe shaguna da shugaban KAROTA yayi a kasuwar waya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Lamarin farko ya auku ne a ranar Lahadi a Hausawa New layout a kwaryar jihar. An tattaro cewa, a kalla shaguna dari da hamsin rusau din ya shafa.

An tattaro cewa, Dan Agundi ya jagoranci motoci biyar na Anti-Daba na rundunar 'yan sandan wurin rushe shagunan wadanda kadarorin da ke ciki suka kai darajar miliyan dari a kasuwar Bello Kano da ke Farm Center a Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Nura Shehu, daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya ce, Dan Agundi ya rushe musu shaguna a ranar da suka yi taro da shi.

"A ranar Laraban mun yi taro da Baffa Dan Agundi kan wasu shaguna da ke filin da yayi ikirarin nashi ne. Ya ba mu kwana biyu kan mu kwashe kadarorinmu kuma mu tashi ko kuma ya rushe.

Kara karanta wannan

Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas

“Amma a wannan ranar, an rushe shagunanmu cikin dare. Na rasa kadarorin da ke cikin shaguna biyu da na mallaka wanda sun wuce naira miliyan ashirin da biyar," Shehu yace.

Sani Yakubu, wanda ya rasa kusan kadarorin miliyan goma sha hudu, ya yi bayanin abinda ya faru da shi.

"Tabbas mun yi taro da shi wurin karfe takwas na dare kuma ya sanar da mu cewa za mu iya kwashe kayanmu cikin dare. Akwai kusan shaguna dari biyu da rumfuna a wurin.
"Kwatsam aka kira ni da safiya cewa an rushe mana shagunanmu. A nan na iso na ga babu kadarori na ko daya," yace cike da hawaye.

Alkassim Musa, wanda yace ya na daga cikin jama'ar da suka fara ganin mummunan lamarin a sa'o'in farko na Alhamis, ya ce ya ga wayoyi masu yawa da aka barnatar da sauran kadarori.

Sai dai a yayin da aka tuntubi Dan Agundi, ya ce filin ba nashi bane, sai dai masu rumfunan ne suka shiga filayen wasu.

Kara karanta wannan

An kama miji da mata da suka hada kai don siyar da ‘ya’yansu mata kan N700,000

Dan Agundi ya kara da cewa, a watan da ya gabata ne hukumar habaka birane ta jihar Kano ta sanar da 'yan kasuwan kuma ta basu notis kan cewa su bar shagunan, lamarin da suka yi kunnen uwar shegu da shi.

Amma kuma, Baffa Dan Agundi ya ki bayyana waye mai filin duk da matsa masa da aka yi kan cewa ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: