Garba Shehu: Buhari ya cancanci jinjina kan yadda ya shawo kan matsalar tsaro
- Hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa ya dace 'yan Najeriya su jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Shehu wanda yayi jawabi a taron cikar FUDMA shekaru goma, ya ce Buhari ya shawo kan matsalar tsaro a kasar nan
- Ya kafa misali da rikicin makiyaya da manoma wanda shugaban ya fitar da tsarin yin wurin kiwo a jihohin Najeriya a matsayin mafita
Katsina - Mallam Garba Shehu, babban mai bayar da shawara ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan bangaren yada labarai, ya ce ya dace a jinjina wa shugaban kasan kan kokarinsa na shawo kan rikicin manoma da makiyaya.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Shehu ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin gabatar da jawabi kan kalubalen labaran bogi wanda yayi a bikin murnar cikar jami'ar tarayya ta Dutsin-Ma shekaru goma a Katsina.
"Sanannen abu ne cewa mulkin Buhari ne kadai gwamnatin Najeriya ta kawo hanyar shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya a duk shekarun da muka kwashe bayan samun 'yancin kai.
"Barazana ga farar hula da kuma zaman lafiya tsakanin kabilu da addinai daga rikicin manoma da makiyaya, 'yan bindiga da kuma rikicin filaye abubuwa ne da gwamnatin Buhari ta mayar da hankali a kai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba daidai bane mutum ya yi tunanin cewa gwamnati ba ta yin komai domin shawo kan matsalolin nan a kasar nan."
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya kara da cewa:
“Da farko, akwai kokarin da ake yi na gina wuraren kiwo domin shawo kan matsalar kiwo a sarari, lamarin da ya ke kawo fadan makiyaya da manoma.
"Wannan tsohuwar matsala ce da gwamnatin Najeriya ke fuskanta tun kafin samun 'yancin kai. Amma kuma, ana kokarin shawo kan ta a kowanne mataki na jihar.
"Don haka ya zama dole gwamnonin jihohi su nuna sun shirya kawo cigaba a bangaren. Gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsarin tun shekarar da ta gabata domin shawo kan matsalar."
Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza
A wani labari na daban, babban Bankin Najeriya ya sanar da sabon shirin lamuni ga wadanda suka kammala karatun jami'a da kwalejojin fasaha da ke son kafa kasuwanci, yana mai cewa matakin wani bangare ne a kokarinsa na yaki da rashin aikin yi a kasar.
Bankin ya ce za a aiwatar da shirin lamunin ne a karkashin shirin sa na Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES).
A cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar ta shafinsa na Facebook ya ce:
“Babban bankin na CBN, a matsayin wani bangare na manufofin sa na magance hauhawar rashin aikin yi ga matasa da zaman banza, ya bullo da Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES) don samar da canji mai kyau tsakanin daliban da suka kammala karatun digiri na kwalejojin kimiyya da jami’o’i a Najeriya, daga neman ayyukan gwamnati zuwa kasuwanci."
Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari
Asali: Legit.ng