Abin Sha'awa: Kofur a Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Kammala Digirin Digirgir

Abin Sha'awa: Kofur a Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Kammala Digirin Digirgir

  • Nnaji Chibueze, wani kofur din hukumar ‘yan sandan Najeriya (NPF), ya kammala digirin digirgir a jami’ar jihar Abia (ABU)
  • Kofur din ya kammala karatun ne a ranar yayen dalibai kashi 27 da 28 da aka hada aka yi a cikin jami’ar wacce take a yankin kudu maso gabas
  • Yayin tattaunawa da manema labarai ya bayyana yadda ya yi karatun cikin mawuyacin hali kuma shi ne mutum na farko da ya yi digirin digirgir a matsayin dan sanda a kauyensu

Jihar Abia - Wani Kofur din rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF), Nnaji Chibueze ya kammala digirin digirgir a jami’ar jihar Abia (ABU), The Cable ta ruwaito.

An yaye Kofur din bayan ya kammala karatun nasa ne a wani taron yaye dalibai na 27 da 28 da aka hada a jami’ar.

Kara karanta wannan

'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblisa ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

Abin Sha'awa: Kofur a Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Kammala Digirin Digirgir
Kofur din 'Yan Sanda da ya yi digirin digirgir. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Gidan talabijin din ABN da ke kudu maso gabas ya wallafa bidiyon jawabinsa a taron yayen, inda kofur din ‘yan sandan ya ce ya shiga mawuyacin hali lokacin da ya fara karatun digirin digirgir din

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kafa tarihi a kauyensu

Kamar yadda ya bayyana:

“Ina matukar farin cikin ganin wannan ranar saboda na fara karatun nan a cikin mawuyacin yanayi.
“A lokacin ban taba tunanin zan iya ganin karshen karatun ba, amma Ubangiji ya ci gaba da ba ni dama har na kai yau.
“Ina farin kasancewa mai digirin digirgir kuma ni ne na farko a kauyenmu da na kafa wannan tarihin a matsayi na na dan sanda saboda yardar da mutane su ka yi cewa ‘yan sanda ba sa karatu mai zurfi.”

Ya ce ya fara tun daga farko ne duk da bai samu wani mai tallafa masa ba, ya jajirce wurin adana ‘yan kudadensa tun da ya fara aiki don ganin ya kai wannan matsayin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Nasarawa: APC bata shirya faduwa a 2023 ba, muna da shiri mai kyau

Ya fara aikin ‘yan sanda a 2012

Kamar yadda ya bayyana wa ABN TV, Kofur din ya fara aikin ‘yan sanda a 2012 kuma dan asalin Umuezibuoko Umualu ne da ke karamar hukumar Isuizor a jihar Enugu.

Ya fara karatun firamarensa a makarantar firamaren Odorbia a Umuezibuoko Umualu, Enugu a 1994 sannan ya kammala a 1999.

Ya cigaba da makarantar sakandare inda ya kammala a 2005 a Community Secondary School da ke Ihaohuala, Enugu.

Ya ci gaba da karatunsa a cibiyar ilimi ta Ecumenical a 2005/2006 inda ya yi karatu a fannin siyasa kuma ya gama da sakamako mai kyau.

Ya kammala digirinsa na farko a jami’ar jihar Enugu ta kimiyya da fasaha (ESUT) a 2010 sannan ya kammala digrinsa na digir a fannin ilimi da tsare-tsare a ABU kafin ya ci gaba da digirin digirgir a fannin ilimi na harkar tsare-tsare da tattali.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

Kara karanta wannan

Buni ya bayyana dalilai 5 da suka sanya Buhari kai babban taron APC watan Fabrairun 2022

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164