Na yi farin ciki da aka kama ni, na san laifi na ke yi, in ji mai kaiwa 'yan bindiga bayanan sirri a Zamfara

Na yi farin ciki da aka kama ni, na san laifi na ke yi, in ji mai kaiwa 'yan bindiga bayanan sirri a Zamfara

  • Wani kasurgumin mai kai wa yan bindiga bayanai da aka kama a Zamfara ya ce ya gayyaci yan bindigan ne kauyen Wanke don su sace shanu 240
  • Abubakar Babuga ya ce sun yi yarjejeniya za a bashi kasonsa cikin shanun amma ba a bashi ba har ta kai ga an kama shi
  • Ya kuma bayyana cewa ya yi farin ciki da aka kama shi domin ya san abin da ya ke aikatawa laifi ne ya kuma nemi afuwar jama'a

Zamfara- Hatsabibin mai kai wa 'yan bindiga bayannan sirri, Babuga Abubakar ya amsa cewa shine ya gayyaci 'yan bindigan su kai hai kauyen Wanke a karamar hukumar Gusau domin su sace wasu shanu 240.

Rundunar yan sandan Zamfara tare da rundunar FIB/STS daga hedkwata a Abuja karkashin jagorancin DSP Hussaini Gimba, a baya sun yi holen wanda ake zargin a Gusau, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kada ka manta da marayun arewa yayin rabon N250m: Ƙungiyar arewa ga Davido

Na yi farin ciki da aka kama ni, na san laifi na ke yi, in ji mai kaiwa 'yan bindiga bayanan sirri a Zamfara
Mai kai wa yan bindiga bayannan sirri a Zamfara da aka kama. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara Mr Ayuba Elkanna ya ce an kama wanda ake zargin ne da taimakon bayyanan sirri da aka samu game da shi.

Wanda ake zargin ya amsa cewa ya kai wa yan bindigan bayanin ne da yarjejeniyar cewa za su bashi kasonsa na shanun satar amma bai samu komai ba tun kafin a kama shi.

Ya ce yana zaune ne a Azara a jihar Nasarawa duk da cewa ainhinsa dan Zamfara ne, ya kara da cewa ya yi farin cikin da aka kama shi domin ya san abin da ya ke yi babu kyau.

A bani dama in koma daji in roki yan bindiga su dawo da shanun da suka sace

Wanda ake zargin ya ce:

"Zan yi farin ciki idan yan sanda za su bani dama in tafi daji in roki barayin shanun su dawo da shanun da suka sace.

Kara karanta wannan

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

"Ina neman afuwa daga wadanda na yi wa laifi sakamakon abubuwa marasa kyau da na yi. Ya zama dole in fada gaskiya domin na zama tamkar kyarkyeci da rigar tinkiya."

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164