Za mu hana komai motsi a kasar: NANS ta gargadi gwamnati kan karin kudin man fetur

Za mu hana komai motsi a kasar: NANS ta gargadi gwamnati kan karin kudin man fetur

  • Kungiyar dalibai ta kasa, NANS ta yi barazanar rufe kasar matsawar gwamnatin tarayya ta tabbatar da sabon farashin man fetur
  • Kungiyar daliban ta nuna rashin amincewarta da shirin gwamnatin tarayya na biyan ‘yan Najeriya miliyan 40 naira dubu biyar a matsayin kudin mota idan an tabbatar da sabon farashin man
  • Yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, shugaban NANS, Kwamaret Sunday Asefon ya ce za su shirya da dalibai miliyan 41 da ke kasar nan zasu yi zanga-zanga

FCT, Abuja - Kungiyar dalibai ta kasa, NANS ta yi barazanar rufe kasar nan matsawar gwamnatin tarayya ta tabbatar da sabon farashin man fetur, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar daliban ta nuna rashin amincewarta da shirin gwamnatin tarayya na biyan ‘yan Najeriya miliyan arba’in N5,000 idan farshin man ya tashi a matsayin kudin mota.

Kara karanta wannan

Shirin kidaya yawan yan Najeriya zai lakume sama da Biliyan N190bn a 2022, Majalisa

Yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, shugaban NANS, kwamaret Sunday Asefon ya ce kungiyar zata shirya da mambobinta miliyan arba’in da daya dake fadin kasar nan don su yi zanga-zanga.

Za mu hana komai motsi a kasar: NANS ta gargadi gwamnati kan karin kudin man fetur
Kungiyar daliban Najeriya NANS ta gargadi FG game da shirin karin kudin man fetur. Hoto: Reuters
Asali: UGC

Ministan kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ta bayyana shirin gwamnati na cire tallafin man da kuma biyan N5,000 ga talakawan Najeriya miliyan arba’in kudin mota.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asefon ya ce kada a kai ‘yan Najeriya bango

Asefon ya kula da halin da kasa take ciki na talauci inda yace gwamnati bata kyauta ba da take shirin cire tallafin ba tare da jin ta bakin mutane ba.

Ya kwatanta shirin a matsayin hanyar da gwamnati zata tatsi kudi ta ko wacce hanya da kuma takura wa kananun ma’aikata ba tare da tunani ba.

Kamar yadda yace:

“Yan Najeriya su na matukar wahala. Suna kuka na fili da na zuci duk saboda tsananin rayuwa. Ana gwada hakurin ‘yan Najeriya ne.

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

“Ina ba gwamnati shawara akan kada ta zake wurin ci gaba da cutar da ‘yan Najeriya.
“Idan aka ci gaba da jan zaren da tsawo zai tsinke. Dama kuma kowa a fusace yake. NANS ta ji dadin yadda kungiyar kwadago da ma’aikata ta nuna rashin amincewarta akan karin kudin man.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164