Zamfara: 'Yan bindiga sun tayar da wani ƙauye bayan sun yi wa mutum 7 kisar gilla
- Rahotanni sun bayyana yadda ‘yan bindiga suka kori mazauna kauyen Yan Buki da ke karkashin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara
- Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da rana inda aka samu bayanai akan yadda suka halaka mutane bakwai yayin farmakin sannan su ka yi garkuwa da wasu
- Wani mazaunin kauyen ya ce akwai wadanda su ka tsaya su na harbe-harbe yayin da wasu su ke bi gida-gida su na binciko mutanen da su ka boye
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun fatattaki wasu mazauna kauyen Yan Buki da ke karamar hukumar Zurmi da ke jihar, Premium Times ta ruwaito.
Sakamakon farmakin sun halaka mutane bakwai sannan sun yi garkuwa da wasu mutanen a ranar Alhamis da rana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin wata tattaunawar da BBC Hausa wacce Premium Times ta gani, wani mazaunin kauyen ya bayyana yadda ‘yan bindigan su ka yi dirar mikiya da tsakar rana.
Ya ce sun yi garkuwa da fiye da mutane hamsin
A cewarsa:
“Sun zo da misalin karfe 12pm sannan su ka dinga harbe-harbe. Wasu su na harbi yayin da wasu suka bi gidaje su na binciko jama’an da su ka boye. A nan suka binciko mata hamsin da yara su ka wuce dasu daji.”
Ya kara da bayyana yadda su ka banka wa wasu shaguna wuta tare da rumbunan da aka adana kayan abinci.
Majiyar ta shaida cewa:
“Bayan tafiyarsu, mun kirga gawawwaki bakwai ciki har da na kanina. Sun harbe shi a gabana. Daga cikin gidansa su ka fito dashi sannan su ka harbe shi a baya da wuya.”
Ya shaida yadda sauran mazauna kauyen su ka tsere Gusau, babban birnin jihar.
Sauran mazauna kauyen duk sun tsere
Har yanzu dai Premium Times bata tabbatar da gaskiyar maganganun wannan mazaunin ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu bai amsa kiran wayar da BBC Hausa su ka yi masa ba, sannan bai bayar da amsar sakon da suka tura masa ba.
Zurmi na daya daga cikin kananun hukumomi jihar Zamfara ne wadanda ta’addanci ya addaba.
Ta na da iyaka da Jibia, Batsari da kuma dajin Rugu da ke jihar Katsina kuma tana da iyaka da karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.
Zamfara: Gwamnati ta rufe wasu gidajen biredi da man fetur da ke yi wa 'yan bindiga aiki
A wani labarin, kwamitin tsaro na gwamnatin jihar Zamfara, a ranar Laraba, ta bada umurnin a rufe wani gidan mai da gidan biredi da ke kananan hukumomin Gusau da Tsafe a jihar, The Cable ta ruwaito.
Abubakar Dauran, shugaban kwamitin ne ya bada wannan umurnin jim kadan bayan jami'an tsaro sun kama wasu mutum hudu da ake zargi da sayarwa yan bindiga biredi da man fetur.
Dauran, wanda kuma mashawarci na musamman ne kan harkokin tsaro ga Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, ya ce an rufe gidan man da ke Tsafe ne saboda sayarwa yan bindiga abokan huldarsu man fetur.
Asali: Legit.ng