Za mu iya horas da 'yan sandan mu a Najeriya, PSC ta fada wa kasar Jamus

Za mu iya horas da 'yan sandan mu a Najeriya, PSC ta fada wa kasar Jamus

  • Hukumar kula da walwalan yan sandan Najeriya, PSC, ta fadawa kasar Jamus cewa za ta rika horas da jami'anta a gida
  • Hakan ya biyo bayan tayin da kasar ta Jamus ta yi wa Najeriya ne na cewa a bata yan sanda 30,000 ta kai su Jamus ta ba su horaswa
  • Amma, Hukumar ta PSC ta ce a shirye ta ke ta yi hadin gwiwa da Jamus din domin ganin ko akwai abin da za ta iya koya daga gare ta

Abuja - Hukumar kula da jin dadin yan sandan Nigeria, PSC, ta rundunar 'yan sandan Najeriya za ta bawa jami'an ta horaswa a gida ba sai sun fita kasar waje ba, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban PSC kuma tsohon sifeta janar na yan sanda, Musiliu Smith ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace fasinjoji 5 a hanyarsu ta dawowa daga kasuwa a Neja

Gwamnatin kasar Jamus, a ranar Talata, ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura jami'anta 30,000 domin su tafi Jamus a basu horaswa na musamman kan yadda za su kwantar da zanga-zanga ba tare da makami ba.

Za mu iya horas da 'yan sandan mu da kan mu, PSC ta fada wa kasar Jamus
A gida za mu bawa jami'an mu, PSC ga Jamus. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Amma Smith ya ce Najeriya da Jamus suna da banbancin al'umma da yanayin zamantakewa kamar yadda ya zo a ruwayar ta Daily Trust.

A cewarsa, yana da muhimmanci jami'an yan sanda su samu horaswa a gida domin a tantance su t

un suna da kananan mukamai a rundunar.

Ya ce:

"Sai mun tantance su. Ka san 'yan kasar Jamus din su zo Najeriya. Sun tattauna da gwamnati da wasu hukumomin da abin ya shafa, har yanzu ana cigaba da tattaunawa.
"Gwamnatin kasar a can tana son bamu tallafi don samar da tsaro a kasar mu, kuma a shirye muke mu basu goyon baya, amma dole ne mu fara bawa jami'an mu horaswa a gida."

Kara karanta wannan

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

Ya cigaba da cewa:

"A hankali, idan sun yi tanadi, muna bukatar mu tafi mu ga kayayyakin aikin da suke da shi da irin tsarin da suke amfani da shi domin al'ummomin mu sun banbanta.
"Muna son mu tabbatar akwai abubuwan da za mu iya amfani da su a nan kasar da zai taimaka mana."

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164