Masarautar Dansadau ta yi zaman sulhu da kasurgumin dan bindiga, Ali Kachalla
- Wata Masarauta a jihar Zamfara ta nemawa kanta mafita daga ta'addancin kasurgumin dan bindiga, Ali Kachalla
- Wazirin masarautar ya yi kira ga matasan garin su guji wani abu da zai janyo matsala ga wannan sulhu
- Tun bayan yanke sabis a sassan Zamfara, mutan jihar sun ce har yanzu da sauran rina a kaba
Zamfara - Wazirin Dansadau, Alhaji Mustapha Umar, ya bayyana cewa Masarautar ta yi zaman sulhu da kasurgumin dan ta'adda mai garkuwa da mutane, Ali Kachalla.
Ali Kachalla, yaransa, da Damina (wanda aka kashe) a kwanakin bayan sun addabi al'ummar Dansadau da hare-hare da garkuwa da mutane.
Daily Trust ta nakalto Wazirin masarautar da cewa Kachalla ya amince da sulhun da akayi kuma wannan zai baiwa manoma daman komawa gonakinsu da kuma matafiya masu bin hanyar Gusau-Magami-Dansadau.
Yace:
"Mun gargadi mutanenmu su nisanci duk wani abun da zai zama matsala ga sulhun nan. Mun wahala sosai gaskiya. Muna kira ga dukkan matasa su zauna lafiya don jin dadin kowa."
Wazirin ya bayyana cewa sun sanar da Gwamnatin jihar kan sulhun kuma sun gayyaci jami'anta su ziyarci masarautar don ganewa idanuwansu.
Ya caccaki wasu daidaikun mutane masu yada jita-jita kan abubuwan dake faruwa a Dansadau amma suna zamansu a Abuja da Kaduna.
Rahoton ya kara da cewa Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, DIG Ibrahim Mamman Tsafe, ya tabbatar da cewa lallai zaman lafiya ya dawo Dansadau.
Zamfara: 'Yan bindiga sun tayar da wani ƙauye bayan sun yi wa mutum 7 kisar gilla
Yan bindiga sun fatattaki wasu mazauna kauyen Yan Buki da ke karamar hukumar Zurmi da ke jihar.
Sakamakon farmakin sun halaka mutane bakwai sannan sun yi garkuwa da wasu mutanen a ranar Alhamis da rana.
Yayin wata tattaunawar da BBC Hausa, wani mazaunin kauyen ya bayyana yadda ‘yan bindigan su ka yi dirar mikiya da tsakar rana.
Asali: Legit.ng