Cire tallafin mai da biyan yan Najeriya N5,000: Sai ka rasa wanda ke ba Gwamnatin nan shawara, Dr Adamu

Cire tallafin mai da biyan yan Najeriya N5,000: Sai ka rasa wanda ke ba Gwamnatin nan shawara, Dr Adamu

  • Dr Adamu ya bayyana ra'ayinsa game da shirin da gwamnatin tarayya ke na cire tallafin man fetur
  • Masanin tattali arzikin ya bayyana cewa mutanen dake bukatan tallafin mai sun zarce milyan arba'in
  • A cewarsa, wannan wata sabuwar hanya ce kawai da yunkurin wawuran kudaden al'umma ayi ruba da ciki da su

Malami a jami'ar Nile dake birnin tarayya Abuja, wanda yayi takhassusi a sashen tattalin arzikin man fetur Masani , Dr Ahmad Adamu ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin cire tallafin man fetur.

A hirar da yayi da wakilin Legit Hausa, Dr Adamu ya yi alhinin shirin da gwamnatin tarayya ke yi na cire tallafin mai a irin wannan lokaci.

A cewar Malamin, gwamnatin Buhari tun lokacin da ta hau mulki a 2015 take kame-kame game da lamarin tallafin mai.

Kara karanta wannan

Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN

A cewarsa:

"Dama ita wannan gwamnatin tun da tazo ta kasa samun matsaya kan cewa zata cire tallafin da take bada ko karta cire."
"Idan zaka tuna a farkon hawan litar mai na N87 aka cire tallafin mai akace ya koma N145, mutane suka shiga damuwa, daga N145 ya koma N160 yanzu, kuma har yanzu ana cewa duk wannan wahalan da aka sha a baya, wai har yanzu ashe ba'a cire tallafin ba, za'a kara shan wata wahalan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin nan shawara, Dr Adamu
Cire tallafin mai da biyan yan Najeriya N5,000: Sai ka rasa wanda ke ba Gwamnatin nan shawara, Dr Adamu Hoto: Dr. Ahmed Adamu/Buhari Sallau
Asali: Facebook

Game da lamarin baiwa yan Najeriya milyan 40 tukwuicin N5000 a wata kuwa, Dr Adamu yace abin ya saba tunani.

A cewarsa:

"Sai ka rasa wanda ke baiwa Gwamnatin nan shawara, idan kace zaka baiwa yan Najeriya milyan 40 kudi dubu biyar-biyar, hakan na nufin zaka rika raba N2.4tr a shekara, kuma wannan ya isa kudin da ake biyan tallafin man."

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

"Kuma ba mutum milyan 40 kadai ke bukatan tallafin mai ba, mutanen dake bukata sun fi milyan 40. Mutanen dake bukata sun kai milyan 100 ko fiye da haka."
"Su waye ne mutum milyan 40 din nan?, wa zai tantance wadanda suka cancanta?, idan ni na cancanta kuma ba'a kirga dani ba fa"

Zamu kara kudin mai, amma zamu fara baiwa yan Najeriya N5,000 kudin mota a wata: FG

Ministar kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmad Shamsuna, ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zata cire tallafin man fetur a 2022.

Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.

A madadin wannan tashi, Ministar kudin ta bayyana cewa Gwamnati za ta fara rabawa talakawan Najeriya dubu biyar-biyar a wata matsayin kudin mota.

Zainab ta bayyana hakan ne ranar Talata a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU).

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng