Ba karamin kaunarta nike ba, Matashin da ya auri Ba-Amurkiya 'yar shekara 70
- Matashi mai suna Bernard Musyokiya bayyana irin mahaukacin son da yake yiwa matarsa Deborah Jan
- Bernard Musyokiya dai dan shekara 35 yayinda sabuwar amaryarsa kuwa yar shekara 70 ce kuma tana da 'yaya biyu
- Matashin ya bayyana cewa ya kosa su sheka kasar Amurka inda zai kasance tare da ita kadai su sha soyayyarsu
- Deborah da sabon Angon a Facebook suka hadu
Matashi dan kasar Kenya, Bernard Musyokiya, ya auri Ba-Amurkiya yar shekara 75 Deborah Jan.
Matashin ya jaddada cewa shi fa soyayyar gaskiya yake mata kuma ba don kudi yake ba kamar yadda ake radawa.

Source: UGC
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda suka hadu
Musyoki, wanda dan jihar Kitui ne a Kenya ya bayyanawa jaridar TUKO.co.ke cewa ya hadu da Deborah ne a manhajar Facebook a shekarar 2017.

Kara karanta wannan
Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19
A cewarsa:
"Ni na bukaci mu fara kawance, bayan mako guda, nace mata ta aure ni kuma ta amince."
A 2018, Musoyoki yace ya shirya zuwa Amurka don haduwa da ita amma aka hanashi biza amma bai yanke tsammani ba.
Ya ce a 2020 ya sake neman biza kuma aka sake hanashi.

Source: UGC
Bamu daina tattaunawa ba
Yace basu daina tattaunawa da juna ba har karshen Disamban 2020, matar ta yanke shawaran zuwa Kenya domin haduwa da shi.
Yace:
"Muna bacci a dakuna daban-daban kuma mun yi alkawarin ba zamu yi jima'i ba har sai an daura mana aure."
A ranar 2 ga Febrairu, 2021, aka daura musu aure a Sheria kuma mutane suka shaida.
Ya ce 'yan uwansa sun yi mamaki lokacin da yace zai auri Deborah.
Yan Najeriya sun yi tsokaci:
Fatima Ta Annabi tace:
"Talauci masifane wannn ai iyace sa'ar kakarshi,Allah yakyauta."
Æthëærmu Prësdœr:
Hhhhhh to wlh Koni yadda nake Shan luguden wahala a Nigeria dana samu wacce zatayi wup Dani wallah Ina fecewa

Kara karanta wannan
Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko
Zainab Yusuf tace:
Hmmmm... Ba dole yaso taba, ita ba dole tasoshi ba, Abar kaza cikin gashin ta kawai..
Hauwau Muhammad tace:
Kamar na dankara ashar wallah Wai soyayya nabi soyayya da Dan banzan guda na daushi keyar ta da katako tirrrrr
Salisu Nasiru yace:
Karya yake shege, kudi yabi, tsohuwa saar kakarsa zaice wani yana mugun sonta
Asali: Legit.ng