Luguden wuta: Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram/ISWAP 90, sun damke kasurgumi da suke nema ruwa a jallo
- Hedkwatar tsaro ta bayyana nasarorin da dakarun soji suka samu a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin mako biyu
- Daraktan watsa labarai na HQ, Bernard Onyeuko, yace sojojin sun hallaka aƙalla yan ta'adda 90, sun kame wasu 21
- Yace wani luguden wuta da jirgin yakin sojin yayi kan yan ta'adda, ya kashe adadi mai yawa da ba'a gano ba har yanzu
Abuja - Hedkwatar tsaro (HQ) tace rundunar sojin Operation Hadin kai ta sheke yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 90 cikin mako biyu da suka gabata a yankin arewa maso gabas.
Mukaddashin daraktan watsa labarai na HQ, Burgediya Janar, Bernard Onyeuko, shine ya bayyana haka ga manema labarai yayin da yake jawabi kan nasarorin sojin daga 11 zuwa 25 ga watan Nuwamba.
The Nation ta rahoto Onyeuko na cewa wani luguden wuta da jirgin yakin sojin ya kaddamar kan yan ta'addan a Baga kusa da tafkin Chadi, ya yi sanadin mutuwar adadin mai yawa daga cikin su.
Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno
Ya kara da cewa a ranar 13 ga watan Nuwamba, dakarun sojin sun dakile hari a Askira Uba, inda suka aika yan ta'adda aƙalla 50 lahira, kuma suka lalata makaman su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sojoji sun damke rikakken ɗan ta'adda
Bugu da kari, sojojin sun kwato motocin yaki, da damman alburusai, daga hannuan yan ta'addan yayin da wasu daga cikin jami'ai suka rasa ransu.
Onyeuko ya kara da bayyana cewa gwarazan dakarun sojin sun samu nasarar cafke wani kasurgumin ɗan ta'adda, Haladu Saleh, wanda suka jima suna nema tun shekarar 2018.
Jimulla yan ta'adda nawa aka kashe?
PRNigeria ta rahoto wani sashin jawabinsa yace:
"A waɗan nan ayyukan da sojoji suka yi, akalla yan ta'adda 90 suka aika barzahu, yayin da suka damke wasu 21."
"Sannan kuma makamai 98 da suka haɗa da bindigun AK-47 da alburusai 2,589 ne dakarun sojin suka samu nasarar kwato wa."
"Daɗin daɗawa sojojin sun ceto mutum 7 da akai garkuwa da su, yayin da mayakan Boko Haram 996 suka mika wuya duk cikin makonni biyu."
Luguden wutan sojoji a Katsina
Sojojin Operation Hadarin Daji sun kaddamar da hare-hare ta sama da ƙasa a yankunan dake karkashin ikon su.
Daga cikin inda suka kai rin waɗan nan harin har da kauyukan Runka da Nasarawa a karamar hukumar Safana jihar Katsina.
Hakanam kuma sun samu nasarar damke wasu masu kaiwa yan bindiga kayan aiki, Alhaji Lawal Auwalu, Ibrahim Tayo da kuma Alhaji Dahiru Abubakar.
Cikin wannan lokaci na mako biyu, sojojin sun kaddamar da irin wannan luguden wutan a jihohin Zamfara da Sokoto.
"A jimlace, jami'an sun damke yan ta'adda 12, sun aika da yan bindiga 118 lahira, sannan kuma suka ceto mutum 5 da akai garkuwa da su."
Operation Safe Haven
Kazalika sojojin Operation Safe Haven sun kaddamar da farmaki ta sama da ƙasa a yankunan dake karkashin su.
Dakarun sojin sun kai irin waɗan nan hare-haren a wasu ƙauyukan jihohin Filato da kuma Kaduna.
Sun samu nasarar kubutar da mutanen da aka sace, kuma sun damke masu tada kayar baya kamar Mr John Paul, wanda ke da ma'aikatar sarrafa alburusai.
Operation Whirl Stroke
Rundunar Operation Whirl Stroke ta cigaba da matsawa marasa son zaman lafiya lamba ta kowane ɓangare kuma yana haifar da sakamako mai kyau.
Dakarun sojin dake kula da yankin arewa ta tsakiya sun kai hari a wasu yankunan jihohin Benuwai, Taraba, da Nasarawa kuma sun samu nasarar kwato makamai daga hannun yan bindiga.
A wani labarin na daban kuma Shekih Ahmad Gumi ya sake jagorantar tawagar Likitoci zuwa wani daji a jihar Kogi
Rahotanni sun bayyana cewa Shehin malamin da yan tawagarsa sun je Rugan ne domin tallafawa Fulanin ta bangaren duba lafiya.
Shugaban rugar Fulanin, Ardo Zubairu, ya nuna jin daɗinsa da ziyarar malamin, tare da rokon a gina musu makaranta.
Asali: Legit.ng