Zamfara: Gwamnati ta rufe wasu gidajen biredi da man fetur da ke yi wa 'yan bindiga aiki

Zamfara: Gwamnati ta rufe wasu gidajen biredi da man fetur da ke yi wa 'yan bindiga aiki

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta rufe wasu gidajen biredi da gidan mai a kananan hukumomin Tsafe da Gusau
  • An dauki wannan matakin ne bisa zarginsu da aiki tare da 'yan fashin daji da suka dade suna adabar mutanen jihar
  • Gwamnatin jihar ta yi kira ga al'umma da su rika bawa gwamnatin jihar hadin kai da goyon baya ta hanyar tona masu aiki da 'yan bindiga

Zamfara - Kwamitin tsaro na gwamnatin jihar Zamfara, a ranar Laraba, ta bada umurnin a rufe wani gidan mai da gidan biredi da ke kananan hukumomin Gusau da Tsafe a jihar, The Cable ta ruwaito.

Abubakar Dauran, shugaban kwamitin ne ya bada wannan umurnin jim kadan bayan jami'an tsaro sun kama wasu mutum hudu da ake zargi da sayarwa yan bindiga biredi da man fetur.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Zamfara: Gwamnati ta rufe wasu gidajen biredi da man fetur da ke yi wa 'yan bindiga aiki
Gwamnatin Zamfara ta rufe wasu gidajen biredi da man fetur da ke aiki tare da 'yan fashin daji. Hoto: The Cable
Asali: UGC

Dauran, wanda kuma mashawarci na musamman ne kan harkokin tsaro ga Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, ya ce an rufe gidan man da ke Tsafe ne saboda sayarwa yan bindiga abokan huldarsu man fetur.

Ya kuma ce za a rufe gidan biredin da ke Gusau kan yi wa yan bindigan safarar biredi.

Ya ce:

"Za a rufe gidan biredin da gidan man fetur din nan take.
"An kama wasu daga cikin wadanda ake zargin dauke da jarkoki, galan-galan da tankin jenareta suna siyan fetur domin kai wa yan bindiga a mabuyarsu.
"An kama su dauke da man fetur sun nufi kauyen Yanware da ke karamar hukumar Tsafe, yayin da masu samar da biredin an kama su ne yayin da suke kaiwa wasu mutanen da ake zargi yan bindiga ne biredi a kan babura."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

Ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu yan jihar marasa kishi suke taimakawa yan bindiga duk da irin kokarin da gwamnan ke yi don dakile matsalar kamar yadda The Cable ta ruwaiito.

Shugaban kwamitin ya yi kira ga al'umma su cigaba da bawa gwamnati hadin kai da goyon baya ta hanyar bada bayanai masu amfani kan yan bindigan da masu aiki da su.

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An ritsa da uwa da matar ƙasurgumin dan bindiga, Bokkolo, yayin luguden wuta a Sokoto

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164