Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema
- Gwamnan jihar Anambra ya shiga jerin mutanen da yaki da cin hanci da rashawa EFCC ke nema
- Gwamna Willie Obiano shi ne gwamnan jihar Anambra mai barin gado watanni kadan masu zuwa
- An ayyana sunan gwamnan ne a yau Laraba, amma har yanzu hukumar ta EFCC bata bayyana dalilin sanya sunansa ba
Anambra - Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta sanya Willie Obiano, gwamnan Anambra a cikin jerin sunayen wadanda take sa ido a kai.
Wannan batu ya zo ne watanni kafin Obiano ya bar ofis a matsayin gwamnan Anambra, kamar yadda TheCable ta ruwaito.
A cewar wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Nuwamba kuma zuwa ga kwanturola-janar na hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), hukumar EFCC ta bukaci a sanar da ita duk lokacin da aka ga Obiano na yunkurin fita kasar waje.
Majiyoyi sun shaida wa Channels Tv cewa matakin wata alama ce da ke nuni da cewa hukumar ta yi bincike mai zurfi a kan gwamnan kuma ta yiwu ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa yana shirin tserewa a ranar 16 ga Maris, 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnonin da ke kan madafun iko a Najeriya na da kariya daga fuskantar tuhuma yayin da suke kan mulki.
Fani-Kayode ya yi magana bayan da EFCC ta kama shi kan jabun takardu
A wani labarin, Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya musanta cewa hukumar EFCC ta kama shi.
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama Fani-Kayode a yammacin ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An ruwaito cewa an kama Fani-Kayode daga bisani aka kai shi ofishin hukumar ta EFCC na shiyyar Legas bisa zarginsa da yin magudi da kuma buga jabun takardu.
Asali: Legit.ng