Gwamnatin Najeriya ta umarci dakatar da hakar man fetur a Bayelsa

Gwamnatin Najeriya ta umarci dakatar da hakar man fetur a Bayelsa

  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da kamfanin AEEPCo daga hakar man fetur a karamar hukumar Nembe ta jihar Bayelsa
  • Ma'aikatar muhalli ce ta fitar da sanarwar ta wata takarda da ta fito daga hannun daraktan yada labarna t a ranar Talata
  • Hakan ya biyo malalar mai da ta auku a wata rijiya wacce aka kasa gano bakin ta sakamakon iskar da ta cika wurin hakar

Bayelsa - A ranar Talata da ta gabata, gwamnatin tarayya ta umarci kamfanin AITEO Eastern Exploration and Production Company Ltd, AEEPCo, da su daina hakan man fetur a rijiyoyin jihar Bayelsa.

A wata takardar da daraktan yada labaran ma'aikatar muhalli, Saghir el Mohammed ya fitar, ya ce gwamnati ta bayar da umarnin cewa kada kamfanin ya sake aiki a yankin har sai an kammala bincike dangane da matakan da suka dauka na bai wa rayuka da kadarori kariya.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun yi martani kan wata yarinya da ta ci A a darussan WAEC, ta ci 345 a Post UTME

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kamar yadda yace, an dauka wannan matakin ne domin dakile malalar man fetur a Santa Barbara da ke karamar hukumar Nembe ta jihar Bayelsa.

Gwamnatin Najeriya ta umarci dakatar da hakar man fetur a Bayelsa
Gwamnatin Najeriya ta umarci dakatar da hakar man fetur a Bayelsa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kamar yadda takardar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnatin tarayya ta umarci kamfanin hakar man fetur na AITEO Eastern Exploration and Production Company Limited (AEEPCo) da su dakatar da aiki a yankin har sai an kammala bincike.
"Hakazalika, za a dauka matakan da suka dace wurin tabbatar an bai wa rayuka da kadarori kariya a yankin.
“Idan za a tuna, an samu malalar mai a ranar 5 ga watan Nuwamba wanda ya taba yankin Opu Nembe daga rijiya ta 1 a kudancin filin da ke Santa Barbara."

TheCable ta ruwaito cewa, takardar ta kara da cewa:

“Bayan samun rahoton aukuwar lamarin, an kafa kungiyar bincike da ta hada da National Oil Spill Detection and Response Agency (NOSDRA), Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC).

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

"Hakazalika, ma'aikatar muhalli, wakilan yankin da kamfanin Aiteo sun kafa kwamitin binciken gaggawa a ranar 6 ga watan Nuwamba.
“An kasa kammala binciken saboda an kasa gano asalin inda rijiyar man ta ke sakamakon iskar da ta mamaye wurin. Daga bisani, JIT ta umarci AEEPCo da su rufe duk wata rijiya saboda a dauka mataki kan malalar man."

Idan ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 ba za su iya biyan albashi ba a 2022, El-Rufai

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce matsawar ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba a 2022, Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a Abuja a wani taro na World Bank Nigeria Development Update, na watan Nuwamba 2021, inda yace don gudun faruwar hakan, a shirye gwamnoni suke don amincewa da cire tallafin man fetur din.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

A cewarsa, in har ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashin ma’aikatansu ba a 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng