Da dumi-dumi: Jirgin kamfanin Air Nigeria zai fara tashi a shekara mai zuwa
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana lokacin da jirgin kasuwanci na Najeriya wato Nigeria Air zai fara tashi
- Gwamnati ta sanya watan Afrilun 2022 a matsayin watan da jirgin zai fara aiki a kasar tare da bayyana batutuwan da suka shafi hannun jari
- Gwamnati za ta rike 5% daga ciki, inda aka ba 'yan kasuwan Najeriya da sauran masu zuba hannun jari sauran kason
Abuja - Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa jirgin Air Nigeria zai fara tashi nan da watan Afrilun 2022, The Nation ta ruwaito.
Ministan ya zanta da ‘yan jarida a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na mako wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, a fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
A cewar Sirika, jirgin na kasa zai hada kai ne da wani kamfani, inda gwamnati za ta rike 5%, ‘yan kasuwan Najeriya 46% yayin da sauran 49% za a kebe su ga abokan huldar hada-hadar da za su hannun jari da suka hada da masu zuba jari na kasashen waje.
Ya kuma kara da cewa kamfanin na kasa idan ya fara aiki, zai samar da ayyuka kusan 70,000 ga ‘yan Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun a watan Mayun shekarar nan Hadi Sirika yake bayyana karin haske kan kamfanin jirgin na Nigeria Air da kuma lokacin da zai fara tashi, kamar yadda TheCable ta ruwaito.
Hukumar kwastam ta yi ram da tulin Tramadol a filin jirgin saman dakon kaya
A wani labarin na daban, jami’an hukumar kwastam ta Najeriya a ranar Talata sun kama kwayoyin Tramadol kimanin miliyan 1.5 a filin jirgin saman dakon kaya na jihar Legas, Channels Tv ta ruwaito.
Jami’an hukumar kwastam ta yankin Murtala Mohammed ne suka kama kayayyakin a rumfar shigo da kaya ta SAHCO dake Legas.
Da yake jawabi ga manema labarai, kwamandan yankin Murtala Mohammed, Sambo Dangaladima ya ce duk da cewa ba a kama wanda ake zargi ba, an kama kayayyakin da kudinsu ya kai Naira miliyan 92.3 domin ci gaba da bincike.
Asali: Legit.ng