Mutane sun tarawa mutumin da ya kwashe shekaru 43 cikin kurkuku kudi, N95m, bayan an gano sharri akayi masa
- An yankewa wani mutum mai suna Kevin Strickland hukuncin shekaru 50 a kurkuku kan zargin kashe mutum uku
- Wacce ta bada shaida a kotu ta dawo daga baya ta canza shaidar da ta bada, bayan shekaru 43 mutumin na gidan yari
- An sakeshi bayan shekaru 43 kuma mutane suka tashi tsaye don taimaka masa da kudi bisa zaluncin da aka masa
An saki wani mutumi mai suna Kevin Strickland a kasar Amurka da ya kwashe shekaru 43 cikin gidan yari kan laifin da ba shi ya aikata ba.
Kevin Strickland wanda dan garin Missouri ne a Amurka, ya shaki kamshin yanci ranar Talata, 23 ga Nuwamba, 2021.
Alkali James Welsh ya wanke mutumin daga laifukan da ake zarginsa da su na kisan mutum uku.
A shekarar 1979, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 50.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sharri aka yiwa Kevin Strickland
A jawabin da ya saki bayan sakinsa, mutumin cikin keken guragu ya mika godiyarsa ga lauyoyinsa da wasu da suka sauraresa.
Yace:
"Har yanzu ban yarda ba. Ban taba tunanin wannan ranar zata zo ba."
CNN ta ruwaito cewa daurin da aka yiwa wannan mutum na cikin aka yiwa dauri kan sharri mafi tsawo a tarihin Amurka.
Abinda ya faru aka daureshi a baya
A ranar 25 ga Afrilu, 1978, an harbi mutane hudu kuma mutum uku suka mutu.
Mutum daya da ya rayu, Cynthia Douglas, wacce ta mutu a 2015 ta bayyanawa kotu cewa Kevin Strickland na wajen lokacin da aka harbesu.
Bayan kimanin shekaru 40, ta canza shaidar da ta bada inda tace kuskure tayi.
Kudin da aka tara masa
Bayan sakeshi, Kungiyar Midwest Innocence Project ta samar da shafi GoFundMe domin tara masa kudi N58m domin taimakawa mutumin.
Amma kawo yanzu da muka wallafa labarin, mutane sun tara masa kimanin N95m.
Asali: Legit.ng