Nan da watanni uku ku kara kudin man fetur: Bankin duniya ga Gwamnatin Najeriya
Bankin Duniya ya yi kira ga Gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur da take badawa nan da watanni uku zuwa shida.
Bankin mai baiwa kasashe bashi a rahoton da yayi yace cire tallafin mai na da muhimmanci saboda ba talakawa ke amfana ba.
A cewar rahotonta na shekara WBU, Bankin yace kashi 40% na yan Najeriya basu amfani da kashi 3% na man feturin da ake kawowa Najeriya, masu kudi kawai ke amfana.
Gwamnatin tarayya ta kashe akalla $2.1 billion (N864 billion) kan tallafin man fetur tsakanin Junairu da Satumban 2021.
Rahoton Bankin yace:
"Abubuwan da ya kamata ayi cikin gaggawa a watanni uku zuwa shida masu zuwa sune rage hauhawan tattalin arziki, inganta kudin canji, cire tallafin mai... da kuma inganta manyan ayuka."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bankin Duniya ne na biyu dake bada wannan shawara
Wannan shawara na Bankin Duniya ya biyo bayan shawaran asusun lamunin duniya IMF a karshen mako.
Asusun Lamunin duniya IMF a ranar Juma'a ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur da na wutar Lantarki gaba daya a farko-farkon shekarar 2022.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur da na lantarki zai tashi.
IMF ya bayyana hakan a jawabin da ta saki na ayyukan karshen 2021, inda ya ce cigaba da biyan kudin tallafi man fetur babban hadari ne rana goben tattalin arzikin Najeriya.
Jawabin yace:
"A yanzu dai, rashin tabbas da ake cikin na bukatar a cire tallafin man fetur da wutan lantarki, a sauya yadda akae karban haraji, sannan a inganta lamarin canji."
"Cire tallafin mai da lantarki gaba daya abune da ya kamata ayi da gaggawa, sannan kuma a taimakawa talakawa da wani abu na rage zafi."
IMF ya jaddada cewa lallai a cire wannan tallafi kamar yadda aka tanada a dokar kamfanin man fetur PIA 2021.
Asali: Legit.ng